MDD: Mutane Miliyan 65 Suke Gudun Hijira A Duk Fadin Duniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6982-mdd_mutane_miliyan_65_suke_gudun_hijira_a_duk_fadin_duniya
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce adadin mutanen da tashin hankali da tsangwama ya raba su da muhallinsu da tilasta musu zama 'yan gudun hijira sun kai mutane miliyan 65.3 a duk fadin duniya.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 06:34 UTC
  • MDD: Mutane Miliyan 65 Suke Gudun Hijira A Duk Fadin Duniya

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce adadin mutanen da tashin hankali da tsangwama ya raba su da muhallinsu da tilasta musu zama 'yan gudun hijira sun kai mutane miliyan 65.3 a duk fadin duniya.

A cikin wani rahoto da ta fitar a yau din nan Litinin Hukumar ta UNHCR din ta ce a karshen shekara ta 2015 da ta gabata, sama da mutanen miliyan 65.3 ne a fadin duniya suka zama 'yan gudun hijira ko kuma masu neman mafaka sakamakon rasa matsugunansu sakamakon yake-yake da kuma gallazawar da suka fuskanta a kasashe da kuma muhallinsu.

A bisa rahoton dai mafi yawa daga cikin wadannan 'yan gudun hijrar sun fito ne daga kasashen Syria, Afghanistan da kuma Somalia wadanda suke fama da yake-yake da tashin hankali da hare-haren ta'addanci.

Rahoton ya ce kashi 51 cikin dari na 'yan gudun hijirar kananan yara ne wadanda mafi yawansu an raba su da iyayensu ko kuma suna tafiya ne su kadai. Don haka Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole sai gwamnatoci sun bayar da hadin don magance wannan matsalar.