Priministan Kasar Britaniya Zai Sauka Daga Mulki
(last modified Fri, 24 Jun 2016 08:17:15 GMT )
Jun 24, 2016 08:17 UTC
  • Priministan Kasar Britaniya Zai Sauka Daga Mulki

Priministan kasar Biritaniya David Cameron ya bada sanarwan cewa zai ajiye aikinsa bayan ficewar kasarsa daga tarayyar Turai.

Cameron ya bayyana haka ne a safiyar yau jumma'a a gidansa da ke lamba 10, Downing Street a birnin Londan, ya kuma kara da cewa zai sauka ya jira lokacinda jam'iyyarsa ta Conservative zata gudanar da taronta na gaba.
Cameron ya ce dole ne a mutunta ra'ayin mutanen kasar ta Britania kan zabin da suka yi na barin kungiyar tarayyar Turai mai membobi 28 bayan kasancewa cikinta na tsawon shekaru 43.
Daga karshe tsohon Priministan ya bayyana cewa ba zai iya shugabancin kasar a tattaunawa mai sarkakiya da zata shiga tare da kungiyar ta EU bayan ficewar kasar daga cikinta ba.