Sabunta Takunkumin Kwamitin Tsaron MDD kan kasar Congo
Kwamitin Tsaro na MDD ya sabunta Takunkumin da ya dora wa kasar D/Congo na tsahon shekara guda.
A jiya Alkhamis ne Manbobin kwamitin tsaron na MDD suka kada kuri'ar aminciewa da sabunta dokar takunkumin da a kakabawa Kasar D/Congo na kudi da kuma sayan makamai har zuwa farkon watan Yunin 2017.sannan kuma suka sabinta aikin tawagar MDD dake sa ido kan zartar da doka har zuwa farkon watan Augustan shekarar 2017.
Ita dai wannan doka da Manbobi 15 na kwamitin tsaro na MDD suka amince ta ita ba ta shafi sayar wa Gwamnati makamai da zirga-zirgar su ba, saidai dokar ta shafi wasu Mutane ne a kasar.
A cewar kwamitin tsaron MDD an dauki wannan mataki ne kan wadannan Mutane saboda an samesu da laifin tayar da tarzoma .
Kwamitin tsaron ya bukaci dukkanin kasashen Duniya, musaman ma kasashen yankin da kuma Dakarun tsaro da sulhu na MDD da su bada hadin kai ga kwamitin sanya ido na ganin an tabbatar da wannan doka.
A karshe Kwamitin ya bukaci da a kawo karshen tayar da kayar baya da kungiyoyin 'yan tawayen Ruwanda (FDLR) , yan tawayen D/Congo (ADF) da sauren 'yan tawaye ke yi a kasar