Amurka Ta yi Maraba Da Nasarar Kwato Falluja
https://parstoday.ir/ha/news/world-i7342-amurka_ta_yi_maraba_da_nasarar_kwato_falluja
Amurka ta ce babbar nasara kwato birnin Falluja da dakarun kasar Iraki sukayi daga hannun 'yan ta'adan IS.
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 28, 2016 01:52 UTC
  • Amurka Ta yi Maraba Da Nasarar Kwato Falluja

Amurka ta ce babbar nasara kwato birnin Falluja da dakarun kasar Iraki sukayi daga hannun 'yan ta'adan IS.

Wannan babbar nasara ce kuma abun yabo ne ga dakarun kasar ta Iraki, inji ministan tsaro kasar Amurka Ashton Carter, a wata sanarwa daga mahuntan Washington.

Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin Irakin data kara kaimi wajen kula da dubban 'yan gudun hijira da suka kaurewa muhalansu a birnin saboda barazana tsaro, da kuma duba zarge-zarge dake yaduwa na cewa ana muzgunawa 'yan gudun hijira.

A shekaraen jiya ne Firaminstan Iraki, Haider al-Abadi ya isa birnin Fallouja da dakarun kasar suka kwato daga hannun 'yan ta'adan (IS), wanda shi ma ya danganta da babbar nasara ta dakarun kasar da dukkan al'ummar kasar ke alfahari dashi.

kwato birnin Fallouja daya jima a hannun 'yan ta'adan IS babbar nasara ce ga dakarun Iraki da suka jima suna fafatawa a wannan yankin da nufin tsarkake shi daga duk wata barazana 'yan ta'ada da suka yi kaka-gida a birnin mai mahimmaci dake yammacin Bagadaza babban birnin kasar.