An kai harin ta'addanci a Labanon
Harin ta'addanci a yankin gabashin Baka'a na kasar Labanon ya yi sanadiyar mutuwa mutane 6 da kuma jikkatar Mutane 19.
Tashar Telbijin din Almayadin ta kasar Labanon ta habarta cewa a jijjifin safiyar yau Litinin wasu ababen bashewa hudu sun tarwatse a kusa da cibiyar tsaron kauyen Baka'a na gabashin kasar Labanon, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6 tare kuma da jikkata wasu 19 na daban.
Har ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wani hari na ta'addanci.
A kwai kungiyoyin ta'addanci daban daban a kasar ta Labanon wadanda ke samun goyon bayan wasu kasashen yamma da na Larabawa, lamarin da ya sanya kasar take fuskantar hare-haren ta'addanci cikin shekarun biyu na baya-bayan nan.
Firaministan kasar Tamam Salam ya ce manufar aiyukan ta'addanci a cikin kasar, sanya sabani tsakanin 'yan siyasar kasar, kuma makiyar kasar ta Labanon na ci gaba da yiwa harakokin tsaron kasarbabbar illa.