Birtaniya: Dubban Mutanen London Sun Kutsa Majalisa.
Mazauna birnin London masu adawa da ficewa daga Trayyar Turai Sun yi Zanga-zanga.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ce; dubban masu adawa da ficewar Birtaniya daga tarayyar turai sun yi zanga-zanga zuwa ginin majalisa a jiya talata.
Masu zanga-zangar dai sun rika bada taken yin tiri da Boris Johnson wanda ya jagoranci kamfe din ficewa daga cikin kungiyar turai. Haka nan kuma sun rika bada wani taken na nuna goyo bayansu ga kungiyar ta turai.
A ranar alhamis din da ta gabata ne dai al'ummar Birtaniya su ka kada kuri'ar raba gardama akan ci gaba ko kuma ficewa daga turai, sai masu son a fice daga kungiyar dai su ka yi nasara.
Bayan sanar da sakamakon karshe na kuri'ar, kawukan 'yan siyasar kasar su ka fara rabuwa.
Pira minista Dadiv Cameroon zai yi murabus daga mukaminsa nan da watanni masu zuwa.