Damuwa kan halin da Mutane ke ciki a yankin tabkin Tchadi
Wakilin kungiyar Kai Agajin gaggauwa ta MDD a yankin Sahel ya bayyana damuwarsa kan halin da Mutane ke ciki a yankin Tabkin Tchadi
Mista Toby Lanzer ya ce sama da Mutane miliyon 9 da dubu dari biyu ke bukatar taimakon Majalisar dinkin Duniya daga cikin su kuma sama da Mutane miliyon 4 da dubu dari hudu ne ke fuskantar barazanar karamcin abinci.
Mista Lanzer ya ce shakka babu al'ummar yankin tabkin Tchadin na cikin mawuyacin hali, domin haka wajibi a gaggauta daukan matakan da suka dace na taimakama su.
Yayin da yake bayyana damuwarsa kan rashin isasun ma'aikatan agaji a yankin, mista Toby Lanzer ya ce a kwai bukatar Duniya ta hada kai domin kai agajin gaggauwa a wannan yanki.
Jami'in ya tabbatar da cewa kimanin mutane miliyon 2 da dubu dari biyu ne suka bar gidajensu sanadiyar Harin kungiyar Boko haram da kuma farmakin da Dakarun hadin kai na kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru, Tchadi gami da Benin ke kaiwa kungiyar Boko Haram a yankin.
Mista Toby Lanzer ya ce sama da Mutane miliyon 23,5 ne ke fuskantar karamcin abinci a yankin Sahel daga cikin su miliyon 5, 9 kananen Yara.