Wajabcin Kawo Karshen Tashe-Tashen Hankula A Kasar Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i805-wajabcin_kawo_karshen_tashe_tashen_hankula_a_kasar_siriya
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Siriya ya jaddada wajabcin kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula a kasar ta Siriya.
(last modified 2018-08-22T06:57:49+00:00 )
Feb 15, 2016 13:35 UTC
  • Wajabcin Kawo Karshen Tashe-Tashen Hankula A Kasar Siriya

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Siriya ya jaddada wajabcin kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula a kasar ta Siriya.

A zantawarsa da jaridar The Wall Street Journal ta kasar Amurka a yau Litinin; Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Siriya Staffan de Mistura ya jaddada cewa dole ne a kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula a kasar Siriya. Staffan de Mistura a yayin zaman taron birnin Munich na kasar Jamus an cimma yarjejeniyar ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da sulhu a dukkanin yankunan kasar ta Siriya.

de Mistura ya kara da cewa: Majalisar Dinkin Duniya ba zata takaita da shirin aikewa da kayayyakin jin kai zuwa kasar Siriya ba, dole ne ta taka gagarumar rawa a fagen ganin an kawo karshen rikici da tashe-tashen hankula a kasar.

A zaman tattaunawan da ministocin harkokin wajen kasashe 15 gami da kungiyoyin kasa da kasa suka gudanar kan rikicin kasar Siriya a birnin Munich na kasar Jamus a ranar Alhamis da ta gabata sun cimma daidaiton baki kan daukan matakan kawo karshen yaki a Siriya tare da aikewa da kayayyakin jin kai zuwa yankunan kasar.