Ban Ki-Moon Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Musgunawa Kananan Yara
(last modified Wed, 13 Jul 2016 05:51:39 GMT )
Jul 13, 2016 05:51 UTC
  • Ban Ki-Moon Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Musgunawa Kananan Yara

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya jaddada wajabcin kawo karshen musgunawa kananan yara a duk fadin duniya.

A jawabinsa a zaman taron nuna goyon baya ga kananan yara tare da kare su daga duk wani dabi'ar musgunawa a jiya Talata: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya jaddada daukan matakan kawo karshen duk wani nau'in cin zarafin kananan yara tare da yin kira ga gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu gami da cibiyoyin kasa da kasa kan hada karfi da karfe domin ganin an 'yantar da kananan yara daga mummunan kangin cin zarafin da suke fuskanta a bangarori da dama na rayuwa.

Wannan furuci na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne bayan dan gajeren lokaci da janye sunan kasar Saudiyya daga jerin sunayen kasashen da suka yi kaurin suna a fagen cin zarafin kananan yara musamman kashe-kashen gillar da suke yi wa kananan yara a kasar Yamen sakamakon matsin lambar da ya fuskanta daga Amurka da gidan Sarautar Saudiyya.