Biritaniya : Theresa May, Ta Nada Sabbin Ministoci
(last modified Thu, 14 Jul 2016 11:57:11 GMT )
Jul 14, 2016 11:57 UTC
  • Biritaniya : Theresa  May, Ta Nada Sabbin Ministoci

Sabuwar Firaminsitar Birtaniya Theresa May ta nada Boris Johnson a matsayin ministan harkokin wajen kasar bayan ta kama aiki a jiya Laraba.

Mr. Johnson wanda tsohon magajin birnin London ne, ya kasance jigo wajen ganin al’ummar Biritaniya sun kada kuri’ar ficewa daga kungiyar tarayyar Turai a zaben raba gardamar da akayi cikin watan jiya.

May ta kuma nada Philips Hammond wanda ya rike mukamin ministan harkokin waje a gwamnatin David Cameron, a sabuwar gwamnatin, inda a yanzu ta ba shi ministan kudi sakamakon goyon bayan da ya nuna mata.

Har ila yau, an nada Amber Rudd a matsayin ministan harkokin cikin gidan Birtaniya yayin da aka bar Michael Fallon akan mukaminsa na ministan tsaro.

Kazalika, May ta nada David Davis a matsayin ministan da zai kula da shirin ficewar kasar daga tarayyar turai.