An Bayyana Damuwa kan ci gaba da rikici a gabashin Ukraine
Kakakin Sojin Ukraine ya bayyana damuwarsa ke yadda rikici ke kara tsanani a gabashin kasar
A Jiya Assabar Kakakin Sojin Ukraine Andriy Lysenko ya kira taron manema Labarai a birnin Kiev fadar milkin kasar,inda da farko ya bayyana damursa kan yadda rikici ke kara tsanani tsakanin 'yan tawaye da Sojoji a gabashin kasar, sannan kuma ya ce a ci gaba da hare-haren da 'yan tawayen gabashin kasar ke kaiwa Sojoji a yankin Luhansk, Soja guda ya rasa ransa, sannan kuma wasu 6 na daban sun jikkata.
Har ila yau 'yan tawayen sun yi awan gaba da wani Soja guda a yankin na Luhansk.
Rikici tsakanin Gwamnatin Ukraine da 'yan tawayen gabashin kasar ya yi sanadiyar hallakar mutane sama da dubu 9 tare kuma da jikkata sama da dubu 21 na daban.
A farkon shekarar 2015 din da ta gabata, Gwamnatin Kasar Ukraine tare da 'yan tawayen gabashin kasar sun cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta a birnin Minsk, saidai dukkanin bangarorin biyu na zarkin dan uwansa da karye wannan yarjejjeniya.