Al' Nusra Ta Yanke Alaka da Al 'Qaeda
kungiyar ta'ada ta Al' Nusra a Syria ta sanar da yanke duk wata alaka da babbar kungiyar ta'adanci ta Al 'Qaeda.
Shugaban kungiyar ta Al 'Nusra Abu Muhammad al 'Jolani ya nuna kansa a karon farko cikin wani hoton bidiyo tare da sanar da yanke alakarsu da babbar kungiyar 'yan ta'adan ta Al' Qaeda da suke aiki tare.
Al Nusra dai ta dade tana alaka da Al Qaeda a Syria.
Yanzu dai shugaban kungiyar Abu Muhammad Al Jolani ya yanke alakar tare da canza wa kungiyar suna zuwa Jabhat fatah al Sham, wato nasara akan Syria.
Shugaban ya aiko da sakon ta kafar bidiyo wanda kafar telebijin ta Al Jazeera ta nuna, kuma wannan ne karon farko da shugaban 'yan ta'adan na Al Nusra ya nuna kansa.
An dade dai ana hasashen rabuwar kungiyoyin biyu, kuma kungiyar Al Qaeda ta tabbatar da rabuwarsu da Al Nusra a wani sakon sauti na kakakinta Qaeda Ahmed Hassan Abu Khair.