Tsohon Sakatare Janar Na MDD, Boutros Boutros-Ghali, Ya Rasu
(last modified Wed, 17 Feb 2016 05:45:54 GMT )
Feb 17, 2016 05:45 UTC
  • Butros- Butros Ghali, tsohon sakatare na MDD
    Butros- Butros Ghali, tsohon sakatare na MDD

Butros shi ne mutum na farko da ya fara zama Sakatare Janar na MDD daga kasashen Larabawa

MDD ta sanar da mutuwar tsohon Sakatare Janar dinta, Boutros Boutros-Ghali, wanda ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

Jakadan kasar Venezuala ne mai rikeda shugabancin kwamitin tsaro na MDD Rafael Dario Ramirez ne ya sanar da mutuwar tsohon jami'in.

Mirigayin dai, wanda dan asalin kasar Masar ne, shi ne mutum na farko da ya fara zama Sakatare janar na Majalisar daga kasashen Larabawa.

Boutros-Ghali dai ya zama maga takardar MDD a shekarar 1992 inda ya yi wa'adi daya na shekara biyar a daidai lokacin rikicin Ruwanda da tsohuwar Wugoslabiya.

'Yan kwamitin tsaro na majalisar sun yi shiru na minta daya domin nuna girmamawa ga tsohon Sakatare Janar dinta wanda Allah yayi wa rasuwa jiyya a birnin Alkahira na kasar Masar.