-
Kotun ICC Ta Ja Kunnen 'Isra'ila' Dangane Da Kisan Gillan Al'ummar Gaza
Apr 09, 2018 06:35Babbar mai shigar da kara a kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki (ICC), Fatou Bensouda, ta ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da kashe sama da Palastinawa 30 da cewa akwai yiyuwar a gabatar da maganar a kotun.
-
Rasha:An Yi Wa Sojojin Siriya Kazafi Na Kai Hari Da Makamai Masu Guba
Apr 08, 2018 14:36Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta sanar da cewa harin da aka ce sojojin Siriya sun kai da makami mai guba a garin Douma kusa da birnin Damuscus, ba gaskiya ba ne
-
Faransa:Ci Gaba Da Adawa Na Sayarwa Saudiya Makamai
Apr 08, 2018 14:35A yayin da yarima mai jiran gado na kasar Saudiya ke ziyara a kasar Faransa,an bukaci shugaban kasar Faransa da ya dakatar da sayarwa kasar ta saudiya makamai.
-
Kungiyar Ikhwanul Muslimin Ta Yi Kakkausar Suka Ga Kalaman Yariman Saudiyya
Apr 08, 2018 06:18Kungiyar Ikhwanul Muslimin ta kasar Masar ta yi kakkausar suka ga kalaman yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya kan kungiyar, inda ta bayyana kalaman nasa a matsayin tsagoron karya kana wani kokari na neman darewa karagar mulki ta hanyar neman goyon bayan Sahyoniyawa da Amurka.
-
Amurka: Shugaban Ma'aikatan Fadar White House Ya Yi Barazanar Barin Aikinsa
Apr 08, 2018 02:04Rahotanni daga Amurka na cewa, sakamakon kai ruwa rana da ake yi tsakanin shugaban kasar Amurka da John Kelly shugaban ma'aikatan fadar White House, hakan ya sanya John Kelly din yin barazanar ajiye aikinsa.
-
An Bankado Kudaden Da Muammar Kaddafi Ya Bai Wa Yakin Neman Zaben Sarkozy
Apr 07, 2018 13:44Tashar talabijin din al'Mayadeen ta kasar Lebanon ta ambato mai yi wa tsohon shugaban kasar ta Libya fassara, Miftah Maisury yana tabbatar da bai wa Nicholay Sarkozy kudaden da su ka kai Euro miliyan 20 a 2007
-
Jamus: Wani Mahari Ya Kashe Mutane Da Dama A Garin Münster
Apr 07, 2018 13:41'Yan sandan Jamus sun ce; Harin da wani mutum ya kai da mota ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane 33 a garin Münster
-
Jami'ar Azhar Ta Yi Allah Wadai Da Halin Ko In Kulan Da Ake Nuna Wa Danyen Aikin 'Isra'ila'
Apr 07, 2018 06:48Jami'ar al-Azhar ta kasar Masar ta yi kakkausar suka dangane da irin shiru da halin ko in kula da manyan kasashen duniya da cibiyoyin kasa da kasa suke nunawa irin wuce gona da iri na baya-bayan nan da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa al'ummar Palastinu.
-
Shugaban Iraki Ya Ki Amincewa Da Zaman Sojojin Amurka Na Har Abada A Kasar
Apr 07, 2018 06:48Shugaban kasar Iraki Fuad Masum ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu ba a yanke shawarar barin Amurka ta kafa sansanin sojojinta na dindindin a kasar Irakin ba, yana mai cewa gwamnatin Iraki ba za ta taba bari a mai da kasar ta zamanto wani waje da za a kai wa wata kasa ta makwabta hari ba.
-
Amurka Ta Hana Kwamitin Tsaron MDD Fitar Da Bayani Kan Zaluncin H.K.Isra'ila
Apr 07, 2018 01:58Kasar Amurka ta sake daukan matakin hana kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya fitar da bayani kan matakin wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka kan al'ummar Palasdinu a yankin Zirin Gaza.