-
PEW: Musulunci Zai Zama Addini Mafi Girma A Duniya A Shekarar 2070
Mar 15, 2018 02:07Wata cibiyar bincike da hasashe a kasar Amurka ta bayyana cewa addinin muslunci zai zama addini mafi girma a duniya daga zuwa 2070.
-
An Yi Ganawar Sirri A Tsakanin Majalisar Turai Da Korea Ta Arewa
Mar 14, 2018 15:41Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato wata majiyar turai na cewa shekaru uku kenan ajere da tawagar majalisar nahiyar take yin ganawa da Korea Ta Arewa, dangane da shirinta na Nukiliya
-
Rasha Ta Ja Kunnen Birtaniyya Da Ta Sake Tunani Kafin Kawo Mata Harin Ta Yanar Gizo
Mar 14, 2018 07:36Kasar Rasha ta ja kunnen gwamnatin Birtaniyya da ta sake tunani sosai kafin ta aiwatar da barazanar kai mata hare-hare ta yanar gizo biyo bayan zargin da Birtaniyyan take yi wa Rashan na hannu cikin kokarin kisan gillan da aka yi wa wani tsohon dan leken asirin kasar a London a kwanakin baya ta hanyar amfani da guba.
-
An Sake Zaben Angela Merkel A Matsayin Waziriyar Jamus A Karo Na Hudu
Mar 14, 2018 07:36'Yan majalisar dokokin kasar Jamus sun zabi Angela Merkel a matsayin waziriya kuma shugabar gwamnatin kasar a karo na hudu mai yiyuwa kuma na karshe na mulkinta a kasar.
-
Jami'an Tsaron Kasar Mexico Sun Kame Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Dalibai 43
Mar 14, 2018 03:01Ma'aikatar shari'ar kasar Mexico ta sanar da kame shahararren mai fataucin muggan kwayoyi a kasar da ake zargi da hannu a kashe daliban makaranta 43 a shekara ta 2014.
-
Bakin Haure 'Yan Afrika Fiye Da 16,000 Ne Aka Mayar Da Su Kasashensu Daga Kasar Libiya
Mar 14, 2018 02:53Babbar jami'a mai kula da siyasar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai ta bada labarin cewa: Bakin haure 'yan kasashen Afrika fiye da 16,000 ne aka koma da su kasashensu daga kasar Libiya.
-
Shugaban Amurka Ya Kori Saktaren Harakokin Wajen Rex Tillerson
Mar 13, 2018 15:33Shugaban Amurka Donald Trump ya kori sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson daga mukaminsa.
-
Rasha Ta Ce Za Ta Mayar Da Martani Idan Amurka Ta Kai Hari Siriya
Mar 13, 2018 07:47Wani babban jami'in sojin kasar Rasha ya bayyana cewar sojojin Rashan za su mayar da martani ga duk wani harin da sojojin Amurka za su kai kasar Siriya matukar dai harin ya zamanto barazana ga rayuwar sojojin Rashan da suke Siriya.
-
Hadarin Jirgin Sama Ya Yi Ajalin Mutum 49 A Nepal
Mar 13, 2018 02:22Akalla mutane 49 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, in da 23 suka jikkata a hatsarin jirgin saman fasinjan a kusa da filin jirage na birnin Kathmandu da ke Nepal.
-
Amurka Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Yaki Da Ta'addanci
Mar 13, 2018 02:22Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce Kasarsa za ta ci gaba da tallafawa Najeriya a fanonin da suka shafi yaki da ta'addanci dama ababen more rayuwa.