-
Rundunar Kawancen Amurka Ta Yi Furuci Da Kashe Fararen Hula 841 A Kasashen Siriya Da Iraki
Feb 23, 2018 01:59Rundunar gamayyar kawance da ke yaki da ta'addanci a kasashen Siriya da Iraki karkashin jagorancin kasar Amurka ta yi furuci da cewa: Tun daga farkon kafa rundunar a shekara ta 2014 zuwa karshen watan Janairun wannan shekara ta 2018 ta kashe fararen hula 841 bisa kuskure.
-
Araqchi: Iran Za Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya Idan Ya Zamana Babu Amfanin Da Take Samu
Feb 22, 2018 14:10Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar za ta fice daga yarjejeniyar nukiliya matukar dai ya zamana ba ta amfanuwa da wani abu daga cikin abin da aka cimma sakamakon barazanar da Amurka take ci gaba da yi wa kamfanoni da cibiyoyin musayen kudade da suke son mu'amala da ita.
-
'Yan Majalisar Birtaniyya Sun Bayyana Adawarsu Ga Ziyarar Yarima Mai Jiran Gadon Saudiyya
Feb 22, 2018 14:09'Yan majalisar Birtaniyya su ashirin da biyu sun bayyana adawarsu ga ziyarar da Yarima mai jiran gado na Saudiyya zai kai kasar lamarin da ya kara karfafa adawar da wasu kungiyoyi da 'yan siyasar Birtaniyyar suke ga wannan ziyarar.
-
Adawar Rasha Kan Kakabawa Iran Takunkumi A Kwamitin Tsaron MDD.
Feb 22, 2018 02:01Wakilin kasar Rasha a Majalisar dinkin duniya ya ce ba za su amince da duk wani kokari da kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya ke yi na kakabawa Iran takunkumi ba, bisa zarkin tana baiwa kungiyar Ansarullah ta kasar yemen makamai
-
Tashin Nakiya Ya Hallaka Sojojin Faransa Biyu A Mali
Feb 22, 2018 01:59Ministan tsaron kasar Faransa ta sanar da hallakar sojojin kasar sa biyu sanadiyar tashin nakiya yayin motar su ke ficewa a kasar Mali.
-
Birtaniya: 'Yar Majalisa Kuma Tsohuwar Minista Ta Yi Suka Kan Nuna Kyama Ga Musulmi
Feb 21, 2018 14:02'Yar majalisar dokokin kasar Birtaniya kuma tsohuwar minista a kasar Sayeed Warsi, ta yi kakakusar suka dangane da yadda ake nuna kyama ga musulmi a kasar Birtaniya.
-
Koriya Ta Arewa Ta Soke Ganawa Da Sakataren Amurka
Feb 21, 2018 02:24Mahukuntan Pyongyang, sun soke wata ganawa da aka shirya wasu manyan jami'an kasar zasu yi da sakataren gwamnatin Amurka, Mike Pence, a daura da gasar Olympics ta hunturu a birnin Pyeongchang, na Koriya ta Kudu.
-
Abbas Abu Mazin Ya Dora Wa Birtaniya Alhakin DUkkanin Abin Yake Faruwa A Palasdinu
Feb 20, 2018 15:31Shugaban na Palasdinawa ya ce; Alkawalin Balfour da Birtaniya ta yi shi ne tushen abin da yake faruwa da al'ummar Palasdinu da kuma mamaya
-
Kwamandan Sojojin Labanon: Za Mu Mayar Da Martani Ga Duk Wani Wuce Gona Da Irin 'Isra'ila'
Feb 20, 2018 01:46Babban kwamandan sojojin kasar Labanon, Janar Joseph Aoun, ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa lalle za a mayar mata da martani ta dukkanin hanyar da ta sawwaka matukar ta kawo wa kasar Labanon din hari.
-
Muhsin Rezai: Isra'ila Za Ta Debi Kashinta A Hannu Matukar Ta Kawo Wa Iran Hari
Feb 19, 2018 07:33Babban sakataren majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci na Iran kuma tsohon babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Muhsin Rezai ya bayyana cewar haramtacciyar kasar Isra'ila za ta debi kashinta a hannu matukar ta kawo wa Iran hari.