-
Amurka : An Kai Hare-haren Bam A birnin New York
Dec 11, 2017 12:01'Yan sanda a birnin New York na Amurka sun ce mutum hudu ne suka raunana sakamakon fashewa wasu abubuwa a tashar jirgin kasa ta Times Square dake yankin Manhattan.
-
Vatican: Matakin Trump Dangane Da Birnin Quds Zai Kara Dagula Lamurra Ne Kawai
Dec 11, 2017 08:21Tsohon ministan harkokin waje na Vatican Pietro Parolin ya bayyana cewa matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka kan birnin Quds zai kara rikita harkokin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ne.
-
Macron Ya Bayyana Adawarsa Game Da Matakin Amurka Kan Birnin Qudus
Dec 11, 2017 02:46Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana adawarsa da bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar.
-
Bukatar Saktare Janar Na MDD Na Kawo Karshen Hare-Haren Saudiya A Yemen
Dec 11, 2017 02:45Babban saktaren Majalisar Dikin Duniya ya bayyana hare-haren da kawancen Saudiya ke kaiwa kan al'ummar kasar Yemen da wawanci tare da neman kasar ta saudiya ta gaggauta dakatar da kai hare-haren.
-
Sanar Da Nasara Ta Gaba Daya Kan Da'esh A Kasar Iraki, Alama Ce Ta Shan Kashin Siyasar Amurka
Dec 11, 2017 02:12A ci gaba da nasarorin da ake samu a kan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh a yankin Gabas ta tsakiya, firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da kawo karshen kungiyar a kasar Irakin da kuma samun nasara ta gaba a kanta.
-
Amurka Ta Ce: Shugaba Trump Ya Shawarci Kawayen Amurka Kafin Daukan Mataki Kan Qudus
Dec 10, 2017 15:37Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana cewa: Shugaban Amurka Donald Trump ya shawarci kawayen kasarsa a yankin gabas ta tsakiya kafin daukan matakin shelanta Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Shugaban Kasar Venezuala Ya Bayyana Shirin Kasarsa Na Kalubalantar Duk Wani Makircin Kasar Amurka
Dec 10, 2017 15:32Shugaban kasar Venezuala ya jaddada cewa: Al'ummar Venezuala suna cikin shirin kalubalantar duk wani makircin kasar Amurka musamman matakin wuce gona da iri kan kasarsu.
-
MDD: A Kaucewa Kuskuren Lissafi Akan Korea Ta Arewa
Dec 10, 2017 04:09Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da bayani da a ciki ya bayyana wajabcin bude kafar tataunawa da Korea ta Arewa domin rage zaman dar-dar a yankin.
-
Shugaban Kiristoci Kibdawa Na Masar Ya Soke Ganawa Da Mataimakin Shugaban Amurka Saboda Batun Qudus
Dec 09, 2017 13:30Paparoman Kibdawan kasar Masar, Paparoma Tawadros II ya soke shirin ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da a baya aka shirya yi a wani lokaci a watan nan a birnin Alkahira don nuna rashin amincewarsa ga matsayar da shugaban Amurkan ya dauka na bayyanar birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Firayi Ministan Iraki Ya Sanar Da Kawo Karshen Yaki Da Kungiyar Daesh A Kasar
Dec 09, 2017 13:30Firayi ministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da kawo karshen yakin da gwamnatin kasar take yi da kungiyar ta'addancin nan ta Daesh a kasar bayan nasarar da dakarun kasar suka samu na kwato dukkanin yankunan da 'yan ta'addan suke rike da su a baya.