-
Rasha Ta Soki Kawancen Da Amurka Ta Ke Jagoranta Na Yaki Da Ta'addanci
Nov 29, 2017 08:41Wakilin Kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ya ce; kawancen yana da rauni wajen musayar bayanan asiri dangane da 'yan ta'adda ko kuma farautarsu.
-
Martani Game Da Sabon Gwajin Makami Mai Linzami Korea ta Arewa
Nov 29, 2017 02:53Sabon gwajin makami mai linzami na korea ta arewa ya ci karo da martanin Amurka da kawayenta
-
MDD:An Fara Gudanar Da Taron Geneva Karo Na Takwas
Nov 29, 2017 02:49Kakakin majalisar dinkin duniya ya sanar da fara taron Geneva karo na takwas domin magance rikicin kasar Siriya.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Gudanar Da Bincike Kan Cin Zarafin Mata A Kasar Myanmar
Nov 28, 2017 15:31Kwamitin yaki da cin zarafin mata na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gwamnatin Myanmar ko kuma Burma da ta gudanar da bincike kan cin zarafin mata musulmin Rohingya.
-
Kungiyar Amnesty International Ta Bukaci A Ba Wa Sheik Isa Qasim Kulawar Likitanci Ta Gaggawa
Nov 28, 2017 01:47Kungiyar kare hakkokin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci gwamnatin kasar Bahrain da ta bari a kai wa shugaban mabiya tafarkin Shi'a na kasar Sheikh Isa Qasim agaji da kulawa ta likita ta gaggawa sakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi.
-
An Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Laifuffukan Yaki UAE A Kasar Yemen
Nov 28, 2017 01:47An shigar da kasar gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a kotun kasa da kasa da mai shari'ar manyan laifuffukan yaki ICC saboda hannun da take da shi cikin hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen da Saudiyya take wa jagoranci.
-
Faransa : Macron Zai Ziyarci Wasu Kasashen Afrika
Nov 27, 2017 03:04Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai fara wani ran gadi a wasu kasashen Afrika uku da suka hada da Bukina faso, Ivory Coast da kuma Ghana a wani mataki na karfafa alaka tsakanin Faransa da Afrika.
-
Rahotanni: Birtaniyya Na Horar Da Sojojin Saudiyya A Asirce Kan Yakan Al'ummar Yemen
Nov 26, 2017 13:49Wata jaridar kasar Birtaniyya ta bayyana cewar sojojin kasar suna gudanar da wani shiri na ba da horo a asirce ga sojojin kasar Saudiyya dangane da yadda za su ci gaba da yaki a kasar Yemen inda sama da mutane 12,000 suka rasa rayukansu kana wasu dubban na daban suka sami raunuka tun bayan da Saudiyya ta kaddamar da hare-hare a kasar ta Yemen a watan Maris na 2015.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Cewa Ana Sayar Da Bakin Haure 'Yan Nigeriya A Kasar Italiya
Nov 26, 2017 04:13Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Ana sayar da mata 'yan Nigeriya da suka shiga kasar Italiya ta barauniyar hanya a matsayin kuyangu domin yin lalata da su.
-
Tarayyar Turai Ta Ba Wa Birtaniya Wa'adin Kwanaki 10 Ta Aiwatar Da Shirye -Shiryen Ficewa Daga Kungiyar
Nov 25, 2017 02:52Shugaban majalisar tarayyar Turai Donald Tusk ya bukaci kasar Birtaniya ta kammala shirye-shiryen ficewa daga tarayyar Turai cikin kwanaki 10 masu zuwa ko kuma tarayyar ta dau mataki a kanta.