-
Manyan Kasashe Masu Arzikin Gas A Duniya Sun Soki Takunkuman Bangare Guda Na Amurka
Nov 25, 2017 02:50Kungiyar manya -manyan kasashe masu arzikin iskar gas a duniya sun yi Allah wadai da takunkuman bangare guda na gwamnatin kasar Amurka kan kamfanonin kasashen kugiyar.
-
AU Ta Zargi Kasashen Turai Da Hannu Cikin Matsalar 'Yan Gudun Hijira Na Afirka
Nov 24, 2017 01:45Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Guinea Conakry, Alpha Konde, ya bayyana cewar kasashen Turai suna da hannu cikin wani bangare na matsalolin da 'yan gudun hijira daga Afirka suke fuskanta a kasar Libiya.
-
Sudan Ta Nemi Taimakon Rasha Kan Bakar Siyasar Amurka
Nov 23, 2017 12:51Shugaba Omar El-Bashir na Sudan wanda kotun hukunta mayan laifuka ta duniya ICC ke nema ruwa a jallo ya fara wata ziyara ta kwanaki hudu a kasar Rasha, mai manufar karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.
-
An Cimma Yarjejeniyar Mayar Da 'Yan Rohingya Gida
Nov 23, 2017 11:44Kasashen Myanmar da Bangaladash sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar ta mayar da 'yan gudun hijirar musulmin Rohingya gida.
-
MDD: Wajibi Ne A Kawo Karshen Killace Kasar Yemen Baki Daya
Nov 23, 2017 03:02Majalisar Dinkin Duniyar ta ce; Ci gaba da killace Filayen saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ruwan Yemen, yana kara taimakawa wajen yaduwar kwalara.
-
Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Ratko Mladich
Nov 23, 2017 02:55Daga karshe dai bayan shekaru 4 da fara shari'a, kotun hukunta masu laifuffukan yaki a birnin Hague ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan Ratko Mladich wanda ya fi shahara da mahaucin Bosnia a jiya Laraba.
-
Shugabannin Iran, Rasha Da Turkiyya Sun Jaddada Kudurin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Siriya
Nov 22, 2017 14:51Shugabannin kasashen Iran, Rasha Da Turkiyya sun jaddada kudurin da suke da shi na ganin an sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Siriya da kuma kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kasar.
-
Kotu Ta Daure Ratko Mladic Daurin Rai Da Rai Saboda Kashe Musulmin Bosniya
Nov 22, 2017 14:51Kotun kasa da kasa mai shari'ar laifuffukan yaki da ke birnin Hague ta daure tsohon kwamandan Sabiyawan Bosniya Ratko Mladic daurin rai da rai a gidan maza saboda samunsa da laifin laifin kisan kiyashi da kuma cin zarafin bil'adama da aka yi wa musulmin kasar Bosniya a shekarun 1992 zuwa 1995.
-
MDD Ta Yi Alawadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai A Najeriya
Nov 22, 2017 07:52Saktare janar na MDD yayi alawadai kan harin ta'addancin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Najeriya
-
Rundunar Sojin Amurka Ta Sanar Da Kashe 'Yan Kungiyar Al-Shabab Ta Somaliya Fiye Da 100
Nov 22, 2017 03:30Rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa: Jirgin saman sojin Amurka ya yi luguden wuta kan sansanin mayakan kungiyar Al-Shabab a shiyar arewa maso gabashin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar ta Somaliya.