MDD: Wajibi Ne A Kawo Karshen Killace Kasar Yemen Baki Daya
Majalisar Dinkin Duniyar ta ce; Ci gaba da killace Filayen saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ruwan Yemen, yana kara taimakawa wajen yaduwar kwalara.
Jami'i mai kula da ayyukan ceto na Majalisar Dinkin Duniya, Jamie McGoldric ne ya bayyana haka a jiya laraba a matsayin martani ga bude wasu hanyoyin shigar da kayan agaji cikin kasar ta Yemen.
A nashi gefen, kakakin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Stephen Dujarric ya bayyana abinda yake faruwa a cikin kasar ta Yeman da "Mufia Babba" sannan ya kara da cewa; Kungiyoyin agaji suna da bukatuwa da a bude dukkanin hanyoyin shiga cikin kasar ta Yemen.
Matsin lambar da Saudiyya ta fuskanta daga kasashen duniya ya sa ta bude tashar jirgin ruwan al-Hdaidah da ke yammacin kasar, sai kuma filin saukar jiragen sama na Sanaa.