-
Zaman Taro Kan Neman Hanyar Magance Matsalar Fitar Da Fatawar Ta'addanci A Duniya
Oct 18, 2017 15:31Manyan malaman addinin Musulunci sun fara gudanar da zaman taron kasa da kasa karo na uku a birnin Alkahira na kasar Masar da nufin neman hanyar shawo kan matsalar fitar da fatawowi da suke yada ayyukan ta'addanci da sunan addinin Musulunci.
-
Mogherini: Yarjejeniyar Nukiliyar Iran, Wata Nasara Ce Ga Duniya Da Kuma Al'ummar Iran
Oct 18, 2017 02:20Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta bayyana cewar yarjejeniyar nukiliyan kasar Iran wata nasara ce ga duniya da kuma al'ummar Iran wanda wajibi ne a kiyaye da kuma ci gaba da aiwatar da ita.
-
Joe Biden: Trump Bai San Komai Kan Yadda Ake Gudanar Da Shugabanci Ba
Oct 18, 2017 02:19Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewar Donald Trump, shugaban kasar Amurkan, bai san komai dangane da yadda ake gudanar da shugabanci ba, yana mai cewa babu abin da Trump din ya kawo in ban da fargaba da damuwa cikin zukatan Amurkawa.
-
MDD Ta Bukaci A Tallafawa Kungiyar G5 Na Sahel
Oct 17, 2017 15:34Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya bukaci kasashen duniya su tallafawa kungiyar kasashen G5 ta yankin sahel a tsakiyar Afrika
-
WFP: Babu Adalci Wajen Raba Abinci A Duniya
Oct 17, 2017 09:00Hukumar abinci ta duniya ( WFP) ta fitar da wani rahoto a jiya talata da a ciki ta bayyana rashin daidaito akan farashin abinci a duniya.
-
Faransa : Trump Ya Jahilci Yarjejeniyar Nukiliyar Iran_Hollande
Oct 17, 2017 02:19Duniya na ci gaba da yin tur da kalamen shugaba Donald Trump na Amurka kan yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce ya ki amuncewa da ci gaba da goyan bayan ta tare da shan alwashin daukan matakin kakabawa Iran din sabbin takunkumi.
-
Ministocin Wajen Kungiyar Tarayyar Turai Sun Sanar Da Goyon Bayan Yarjejeniyar Nuliyan Iran
Oct 16, 2017 14:00Ministocin harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai sun sanar da cikakken goyon bayansu ga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran suna masu cewa kasashensu za su ci gaba da aiki da abin da aka cimma cikin yarjejeniyar.
-
Siyasar Trump Kan Iran Na Kara Tabbatar Da Cewa Amurka Ba Abar Yarda Ba Ce
Oct 16, 2017 01:07A ranar 14 ga watan Yulin 2015 ne, bayan kokari da tattaunawa na tsawon shekaru da nufin cimma matsaya kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran, aka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya (wato kasashen Amurka, Rasha, China, Birtaniyya, Faransa bugu da kari kan kasar Jamus).
-
Jawabin Trump Ya Maida Amurka Saniyar Ware_ Jonh Kerry
Oct 15, 2017 13:12Duniya na ci gaba da yin tur da kalamen shugaban Amurka Donald Trump kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran wacce ya ki amuncewa da ci gaba da goyan bayan ta tare da shan alwashin kakabawa Iran takunkumi.
-
Yawan Mutanen Da Suka Mutu Sanadiyyar Gobarar Daji A Amurka Suna Karuwa
Oct 15, 2017 02:49Hukumar gandun daji ta jihar Califonia a kasar Amurka ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya zuwa jiya Asabar sanadiyar gobarar daji a jihar ya kai 40.