-
Wasu Yan Majalisar Dokokin Amurka Ba Zasu Halarci Bukin Rantsar Da Trump Ba
Jan 17, 2017 08:30Yan majalisar dokokin Amurka 40 ne ya jam'iyyar Democrate suka yanke shawara ba zasu halarci bukin rantsuwar kami aiki na Donal Trump wanda za'a gudanar a ranar 20 ga watan Jeneru da muke ciki ba.
-
Kasar Rasha Ta Dora Laifi Kan Amurka Kan Gasar Kere Makamai Tsakanin Kasashen Yamma Da Ita
Jan 17, 2017 08:29Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta dora laifin gasar tattara makamai wanda bangarorin kasashen yamma da ita Rasha suka shiga a halin yanzu kan gwamnatin kasar Amurka.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Nuna Damuwa Kan Matsalolin Kasar Sudan Ta Kudu
Jan 17, 2017 04:50Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka kan gwamnatin Sudan ta Kudu sakamakon rashin gudanar da bincike domin hukunta masu hannu a take hakkokin bil-Adama a kasar.
-
Merkel, Ta Mayarwa Da Trump Martani
Jan 16, 2017 14:14Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta mayarwa da zababen shugaban kasar Amurka Donald Trump martani dangane da kalamen da yayi na cacakar tarraya Turai.
-
Zabebben Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Ce Akwai Yiyuwan Dagewa Rasha Takunkumai
Jan 16, 2017 08:20Zabebben shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa akwai yiyuwan a dagewa kasar Rasha takunkuman da aka dora mata idan ya karbi iko da kasar.
-
Daraktan CIA Ya Gargadi Donald Trump Da Yayi Taka Tsantsan Kan Abubuwan Da Yake Fadi
Jan 16, 2017 02:20Daraktan hukumar leken asiri ta Amurka (CIA), John Brennan, ya gargadi zababben shugaba kasar Donald Trump da ya nesanci maganganu marasa ma'ana da yake yi, don kuwa a cewarsa hakan lamari ne da zai taimaki harkokin tsaron Amurkan.
-
An Gudanar Da Gangamin Allah Wadai Da Gwamnatin Bahrain A London
Jan 16, 2017 02:20A daidai lokacin da kungiyoyi da manyan 'yan siyasa na kasashe daban-daban suke ci gaba da Allah wadai da hukuncin kisa da gwamnatin Bahrain ta zartar kan wasu matasa uku masu neman 'yanci a kasar, daruruwan membobin kungiyoyin kare hakkokin bil'adama ne suka gudanar da wani gangami a gaban ofishin jakadancin Bahrain din a birnin London don yin Allah wadai da gwamnatin kasar.
-
Musulmin Amurka Sun Bukaci A Hana Wani Mai Kin Jinin Muslunci Halartar Taron Rantsar Da Trump
Jan 15, 2017 15:30Cibiyar musulmin kasar Amurka ta bukaci da a soke sunan wani malamin addinin kirista mai tsananin kiyayya da musulmi daga cikin sunayen mutanen da aka gayyata domin halartar taron rantsar da Trump.
-
Wuta Ta Tashi A Cikin Wani Masallaci A Birnin Washington Na Amurka
Jan 15, 2017 13:41Wuta ta tashi a cikin wani masallaci da ke cikin birnin Washington na kasar Amurka, inda dukkanin kaddarorin da ke cikin masallacin suka kone kurmus, duk kuwa da cewa musumi sun yi iamnin cewa da gangan ne aka saka wutar.
-
An Fara Zanga Zanar Yin All..Wadai Da Trumpm Kwanaki Kafin Ya Karbi Iko Da Amurka
Jan 15, 2017 08:18Masu rajin kare hakkin bil'adama a Amurka sun fara zanga zangar yin All...wadai da zabebben shugaban Amurka Donal Trump kwanaki kafin ya karbi ragamar shugabancin kasar.