An Gudanar Da Gangamin Allah Wadai Da Gwamnatin Bahrain A London
A daidai lokacin da kungiyoyi da manyan 'yan siyasa na kasashe daban-daban suke ci gaba da Allah wadai da hukuncin kisa da gwamnatin Bahrain ta zartar kan wasu matasa uku masu neman 'yanci a kasar, daruruwan membobin kungiyoyin kare hakkokin bil'adama ne suka gudanar da wani gangami a gaban ofishin jakadancin Bahrain din a birnin London don yin Allah wadai da gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran ya bayyana cewar a jiya Lahadi ne daruruwan masu kare hakkokin bil'adama da kuma wasu 'yan kasashen waje suka taru a gaban ofishin jakadancin Bahrain din da ke birnin London don nuna rashin jin dadinsu da zartar da wannan hukuncin da kuma ci gaba da take hakkokin al'ummar Bahrain din da mahukuntan Bahrain din suke yi.
Rahotanni sun ce masu gangamin dai wadanda suke rera taken, la'antar Al Khalifa (mahukuntan kasar Bahrain din) har ila yau kuma sun yi Allah wadai da irin goyon bayan da Birtaniyya take ba wa gwamnatin Bahrain din da kuma kunnen uwar shegun da sauran manyan kasashen duniya suke yi kan danyen aikin da gwamnatin Bahrain din take yi.
A safiyar jiya Lahadi ne dai mahukuntan Bahrain din suka sanar da zartar da hukuncin kisan a kan wadannan matasa uku, masu fafutukan 'yancinsu wato Sami Mushaima, Abbas al-Sami’ da Ali al-Sinkis bisa zargin kai hari da kashe wani jami'in 'yan sanda zargin da matasan suka musanta.