-
MDD Ta Yi Allawadai Da Harin Amurka Kan Fararen Hula A Afganistan
Sep 30, 2016 07:52MDD tayi allawadai da wani harin Amurka a Afganistan daya kashe fararen hula 15 a cikin wannan mako.
-
Kai Kara Saudiyya, Zai Haifar Da Mummunan Sakamako Ga Amurka
Sep 30, 2016 06:57Ma'aikatar harkokin wajen Saudiya ta fitar da wata sanarwa da ke gargadi cewa, kudurin da majalisar dokokin Amurka ta zartas wanda ke nuna goyon bayan iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata sakamakon harin ranar 11 ga watan Satumba da su kai karar gwamnatin Saudiya, zai haifar da mummunan sakamako ga Amurka.
-
Iran: Kungiyar OPEC Ta Dau Matsaya Mai Kyau Dangane Da Batun Hako Mai
Sep 29, 2016 14:36Ministan man fetur na kasar Iran Beijan Zanganeh ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi na'am da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta dauka a zaman da jami'an kungiyar suka gudanar a kasar Aljeriya a jiya Laraba
-
Rasha Ta Yi Watsi Da Barazanar Amurka, Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Gwamnatin Siriya
Sep 29, 2016 14:35Gwamnatin kasar Rasha ta yi alkawarin ci gaba da goyon bayan gwamnatin Siriya da kuma ci gaba da kai hare-haren da take kai wa 'yan ta'adda a kasar tana mai watsi da barazanar da Amurka ta yi mata na dakatar da hadin gwiwan da take yi da Rashan a Siriyan.
-
Siriya / MDD : Akwai Wuya A Tattauna, Muddun Ana kai Farmaki
Sep 29, 2016 08:36Wakilinn musamen na MDD, kan rikicin kasar Siriya, Staffan de Mistura, ya bayyana cewa akwai wuya a ci gaba da tattaunawa kan rikicin kasar Siriya mudun dai ana ci gaba da ruwan bama-bamai a ko ina.
-
Rasha ta mayar da martani kan barazanar Amurka
Sep 29, 2016 02:17Ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta mayar da martani kan barazanar da magabatan Amurka su ka yi na yanke alaka da kasar a kan warware rikicin kasar Siriya.
-
Kungiyar OPEC ta cimma matsaya na rage yawan Man fetur din da take hakowa a kowace Rana
Sep 29, 2016 02:16Manbobin Kungiyar OPEC sun cimma matsaya na rage yawan Man fetur din da suke hakowa a ko wata rana daga ganga milyan 33/24 zuwa ganga milyan 32/5
-
Kungiyar Musulmin kasar Jamus ta bayyana damuwar ta kan ci gaba da hai hare-haren a Masallatai
Sep 29, 2016 02:16Hare-haren baya bayan nan da ake kaiwa kan Masallatai a kasar Jamus yayi sanadiyar bayyana damuwa ga kungiyoyin musulmi na kasar
-
EU Ta Cire FARC Daga Jerin Kungoyoyin 'Yan Ta'adda
Sep 27, 2016 07:27Kungiyar tarayya turai ta cire kungiyar 'yan tawayen FARC ta Columbiya daga cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar kasar.
-
Saudiyya Ta Zabge Albashin Ma'aikatan Kasar Sakamakon Matsalar Tattalin Arziki
Sep 27, 2016 02:20Gwamnatin Saudiyya ta sanar da wasu sabbin matakai na rage albashin ministoci da wasu hakkoki na ma'aikatan gwamnatin kasar da kashi 20 cikin dari don cike gibin kasafin kudin da take fuskanta biyo bayan faduwar farashin mai da kuma kudaden da ta kashe wajen sayo makamai lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar cikin tsaka mai wuya.