-
Wata Tawagar Kwamitin Sulhu Na MDD Na Ziyara A Sudan Ta Kudu
Sep 03, 2016 13:23Wata tawagar kwamitin sulhu na MDD ta fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Sudan ta Kudu da nufin ingiza shawarwarin zaman lafiya a wannan jinjira kasa da rikici ya daidaita.
-
An Kashe Mutane Da Dama A Harbe Harben Da Aka Yi A Amurka A Jiya Jumma'a
Sep 03, 2016 08:27Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran daga Amurka ta bayyana cewa, cibiyar bada rahotannin harbe harbe da bindigogi a kasar ya bada rahoton cewa an kashe ko an raunata akalla mutane 75 sanadiyyar harbi da bandiga a kasar a cikin sa'oi 24 da suka gabata.
-
An Yi Harbe Harbe A Kusa Da Birnin Marsi Na Kasar Faransa Inda mutum Guda Ya Rasa Ransa.
Sep 03, 2016 08:25Majiyar Jandarmari na kasar Faransa a garin Marsi na gudancin kasar ta bayyana cewa wani dan bindiga ya yi harbi ya kuma kashe wani matashi dan shekara 24 har lahira a safiyar yau Asabar.
-
Mutane 12 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Bomb A Kasar Philiphines
Sep 03, 2016 01:04Rahotanni daga kasar Philippine sun bayyana cewa alal akalla mutane 12 sun rasa rayukansu kana wasu kuma sun sami raunuka sakamakon fashewar wani bomb da aka dana a garin Davao, mahaifar shugaban kasar Rodrigo Duterte a jiya Juma'a.
-
An Tsaida Ranar 9 Ga Satumba A Matsayin Ranar Da Za'a Zabi Magajin Ban Ki Moon
Sep 03, 2016 01:03Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da ranar 9 ga watan Satumban nan da muke ciki a matsayin ranar da za a kada kuri'a domin zaban sabon babban sakataren majalisar wanda zai gaji babban sakataren na yanzu Mr. Ban Ki Moon.
-
Venezuela Ta Zargi Amurka Da Shirya Zanga-Zangar Kin Jin Gwamnatin Kasar
Sep 03, 2016 01:02Ministar harkokin wajen kasar Venezuela Delcy Rodríguez ta zargin gwamnatin Amurka da cewa ita ce ta shirya da kuma tsara zanga-zangar baya-bayan nan da masu adawa da gwamnatin kasar suka yi a birnin Caracas, babban birnin kasar Venezuelan.
-
Rasha Zata Maida Martani Ga Shirin Amurka Na Fadada Takunkuman Da Ta Dorawa Kasar
Sep 02, 2016 03:13Kakin fadar shugaban kasar Rasha ya bayyana cewa gwamnatin Putin zata maida martani ga shirin Amurka na fadada tukunkuman tattalin arziki kan kasar.
-
Kasashen Latin Sun Janye Jakadunsu Daga Brazil Don Nuna Fushi Da Tsige Rousseff
Sep 01, 2016 12:50Kasashen Bolivia, Venezuela da Ecuador sun sanar da janye jakadunsu daga kasar Brazil don nuna rashin jin dadi da amincewarsu ga matakin da 'yan majalisar dattawan kasar suka dauka na tsige shugabar kasar Uwargida Dilma Rouseff da suka yi a jiya Laraba.
-
Shugaban Kasar Venezuela Ya Bukaci A Cirewa Yan Majalisar Dokokin Kasar Rigar Kariya
Sep 01, 2016 08:09Shugaban kasar Venezuela ya bukaci ma'aikatar shari'ar kasar ta duba yiyuwan cirewa wasu jami'an gwamnatin kasar, musamman yan majalisar dokoki rigar kariya don gurfana a gaban kulia kan zargin juyin mulkin da zasu shirya masa.
-
Majalisar Dattawan Brazil Ta Goyi Bayan Tsige Dilma Rousseff
Sep 01, 2016 03:12Majalisar dokokin Brazil ta kada kuri'ar tsige Shugaba Dilma Rousseff, wace aka jima ana ta cece-kuce akan zarginta da almudahana a kasafin kudin kasar, koda yake Madam Roussef tana musunta zargin.