Dec 13, 2016 02:11 UTC

Yau Litinin 22-Aazar-1395H.Sh= 12-R-Awwal-1438H.K.=12-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1491 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-R-Awwal-53Kafin hijira, ko kuma shekarar giwaye, bisa wasu ruwayoyi a ranar ce aka haifi manzon Al..(s) a birnin Makka. A bisa wasu kuma an haifeshi ne a ranar Jumma'a 17 ga watan na R-Awwal na shekarar. Don haka ne a nan JMI a kan ware kwanaki 12-17 na watan Rabiul awwal na ko wace shekara a matsayin makon hakin kai tsakanin musulmin duniya. Don haka ne har'ila yau akan gayyace malaman addini da masana zuwa taron makon hadin kai don kusatu da musulman shia da sunna a duniya. Muna taya al-ummar musulmin murnan zagayowan ranar haihuwar fiyayyen halltu.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1437 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-R-Awwal-shekara ta farko na hijirar manzon All..(s) daga makka zuwa madina, mazon All..(s) ya gina masallaci na farko a musulunci a garin Quba kusa da birnin Madina jim kadan bayan hijirarsa daga Makka zuwa madina.

Manzon Al…(s) ya tsaya a garin Quba nay an kwanaki kafin ya shiga birnin Madina don yana jiran Aliyu dan Abitalib (a) ya karaso daga Makka tare da iyalan gidansa don su shiga madina tare. Har'ila yau a wannan masallacin ne manzon All…(s) ya gudanar da sallar jumma'a ta farko a musulunci. A halin yanzu masallacin yana nan a wajen birnin Madina ga duk wanda yake son ziyarar ganinsa.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Decemba-1963M. Kasar Kenya daga gabacin Afrika ta sami 'yencin kanta daga hannun turawan Ingila yan mulkin mallaka. Turawan sun fara mamayar kasar Kenya ne a farkon karni 19 miladiya sannan a shekara ta 1920M sun kammala kafa ikonsu a kasar Kenya. Sai kuma a dai dai lokacin da suka kafa ikonsu ne mutanen kasar Bakaken fata suka fara gwagwarmayan kwatar 'yencin kasar daga hannun turawan karkashin shugabancin Njoma Kenyata. Wannan gwagwarmayan dai ta kai ga kasar ta shiga yakin basasa da turawan a shekara 1953 sannan daga karshe ta tilatawa turawan kafa majalisar dokoki wacce yan kasar ta Kenya suke da babban rinjaye a cikinta, sannan suka zabi Joma Kenyata a matsayin shugaban kasa a shekara ta 1961. Sanna daga karshe karsar Kenya ta sami cikekken 'yenci a shekara 1963.