Ko Kun San na (269) 23 Aazar Shekara ta 1395 Hijira Shamsia
Yau Talata 23-Aazar-1395H.Sh= 13-R-Awwal-1438H.K.=13-Decemba-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 113 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Aazar-1282H.SH. Aka haifi Dr Mahmood Najam-abad wani fitaccen likata dan kasar Iran a nana birnin Tehran. Najam-Abadi ya fara karau a nan Tehran, sannan ya shiga jami'ar koyarwa ta likotoci. Bayan kammalawa sai ya shiga bincike da kuma wallafe likitoci. Banda haka Dr Najam-abadi yana karantarwa a Jami'a ya kuma rubuta da tarjama littafai wadanda yawansu ya kai 45, daga cikin dai ya tarjama littafan likitanci na musulmi da kuma Iran wadanda suka hada da littafan zakariya Razi. Dar Najam-abad ya yaru a shekara ta 1379H.SH
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Decemba-1963M. Sheikh Mahmood Shaltut shugaban Jami'an al-azhar ta kasar Masar ya rasu. An ahife sheikh shaltut a shekara ta 1892 a birnin Eskandaria kuma yana dan shekara 14 ya shiga makarantar koyon addini, sai kuma a shekara 18 ya shiga jami'ar karatun addini a eskandaria. Bayan wani lokaci ya kammala karatu sannan aka zabe shi a matsayin malami a Jami'an sharia a birnin Alkahira. Sai kuma a shekara ta 1958 ya zama shugaban Jami'an al-azhar. Daga cikin ayyuka masu muhimmanci wanda sheikh shaltut yayi shi ne musayar wasiki da Aya. Burujadi shugaban hauza na mazhabar shia a nan Qum da kuma Aya. Sharaffuddeen na kasar Lebanon wanda ya kai ga sheikh Shaltut ya bayyana mazhabar Jaafariya a matsayin mazhaba ta addinin musulunci kamar sauran mazhabobin musuluni ya kuma warewa mazhabar ajujuwa da malamai a cikin jami'an al-azhar.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 13 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Decemban-2003M. Sojojin kasar Amurka wadanda suke mamaye da kasar Iraqi a lokacin sun kama tsohon shugaban kasar Sadam Husaina wani mabuyarsa dake kusa da garin Tikrit daga arewacin kasar. Kasashen Amurka ta Britania dai sun mamaye kasar Iraqi ne a cikin watan maris na shekara ta 2003, suka kuma kifar da gwamnatin sadam Husain daga nan ne ya fara buya, har zuwa lokacinda aka tseginta masu inda tsohon shugaban yake boye a cikin wani rami a kusa da Tikrit. Bayan kama shi dai mutanen kasashen Iran da Kuwait da kuma muatanen kasar da dama sun ji dadi don irin zaluncin da sadam yayi masu. Sadam yah au kan kujerar shugabancin Iraqi a shekara 1979. A shekara 1980 ya mamaye kasar Iran na tsawon shekaru 8, sanna bayan haka ya mamaye kasar Kuwai har zuwa lokacinda aka fitar da sojojinsa da karfi. Daga karshe dai Amurka ta mika shi ga gwamnatin Iraki wacce ta gurfanar da shi ta kuma yanke masa hukuncin kisa kan wasu laifuffuka da ya aikata a lokacinda yakemulki.