Dec 13, 2016 02:16 UTC

Yau Laraba 24-Aazar-1395H.Sh= 14-R-Awwal-1438H.K.=14-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  1374 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-R-Awwal-64H.K. Yazid dan Mu'awiya sarki na biyu daga sarakunan bani umayya ya halaka. Yazid yana dan shekara 37 a duniya ya gaji kujeran babansa kuma a cikin shekaru ukku da watanni 9 da yayi yana sarautar daular musulunci ya aikawa wasu mummunan ayyukan wadanda tarihin duniya ba zata manta da sub a. Da farko dai a shekara ta 61 H.K. ya kasha Imam Husain jikan manzon All..(s) tare da sahabbansa a kasar Karbala na kasar Iraqi. Bayan haka yazid ya halattawa sojojinsa Madinan manzon Alll.. (s) da su yi abinda suka ga dama da mutanen garin na tsawon kwanaku ukku wannan shi ne ake kira waki'ar hurrah, na ukku kuma ya tura sojojinsa da su kona dakin Kaaba a Makka..

Sai dai bayan kisan Imam Husain(a) a karbawa an yi ta samun yan tawaye masu nuna rashin amincewarsu da wannan mummunan aiki. Har'ila yau kissan Imam Husain (a) a karbala ya farkarda al-ummar musulmi kan hatsarinda ke tattare da sarakunan bani ummaya.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 217 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Decemba-1799M.  George Washington shugaban kasar Amurka na farko ya rasu. An haifi George Washington a shekara ta 1732 a jihar Vigenia na kasar ta Amurka, ya kuma taba zama dan majalisart dokoki na jihar . Sannan ya shiga aikin soje ne yana dan shekara ta 22 a duniya. Sai kuma a shekara ta 1775 masu rajin neman 'yencin kasa ta Amurka daga hannun turawan Ingila yan mulkin mallaka wadanda suke mulkin mallaka a kasar, sun zabe George Washington a matsayin babban kwamandan rundunarsu na yaki da yan mulkin mallaka. Sai kuma bayan samun nasara ne a shekarata 1788 aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Amurka na farko bayan samun 'yenci. Shekaru ukku kacal bayan kammala wa'adin mulkinsa na biyu George Washington ya rasu.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Decemba-1981M. Majalisar dokokin HKI wacce ake kira Kenes ta kada kori'ar amincewa da hada yankin tuddan Golan na kasar Syria ya zama bangaren haramtacciyar kasar. Yahudan sun kwace wannan yankin ne a yakin da ta shiga da kasashen larabawa a shekara da 1967. Kasashen sharia da sauran kasashen larabawa sun yi All…wadai da matakin na HKI. Sai dai don irin goyon bayan HKi take samu daga kasashen yamma musamman Amurka haka maganar ta wace. Sai dai har yanzun gwamnatin kasar Syria tana kan bakanta na cewa wannan yankin bangarene na kasarta.