Dec 13, 2016 02:18 UTC

Yau Alhamis 25-Aazar-1395H.Sh= 15-R-Awwal-1438H.K.=15-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  164  da suka gabata a rana irin ta yau wato  15-Decemba-1852M. Aka haifi Henri Becquerel   wani masanin ilmin kimiyar lissafi a birnin Paris na kasar Faransa. Henri ne ya gano wani haske da ake kira X-ray . X-ray dai wani haske ne wanda yake fita daga sinadarin radio active sannan yana da amfani sosai ga bil'adama. Hasken X-ray dai yana ratsa jikuna masu taushi daga cikin har cikin jikin matum, don haka ne ake amfani da shi wajen ayyukan likitanci da dama. Henri ya karbi kyautar Nobel a shekara ta 1902, ya kuma rasu a shekara ta 1908M.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 144 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-R-Awwal-1294H.K. Aka Haifi Mohammad Qazvini malamin tarihi da adabin harshen farisanci a nan Tehran. Qazwini ya fara koyin adabi yana matashi sannan ya fara karatu ilmin kalam a gaban iyayen wadanda suka kasashen masana a wannan fannin. Bayan kamala karatun jami'a Qazvini ya je kasashen Turai inda ya gudanar da bincike mai yawa kan harshe da adabin farisanci. Ya kuma rubuta wasu ilmomi masu yawa wadanda turawan suka ajiye a wuraren ajiyar kayakin tarihi, kuma dakunan ajiye littafai. Muhammad Qazvini ya rubuta littafa da dama daga cikinsu akwai «تاریخ و زندگی در عصر حافظ» . Muhammad qazvini ya rasu a shekara ta 1369 kuma an yi masa kabari a garin Rai dake nan kuda da birnin Tehran.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 41 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Decemba-1975M. Sojojin kasar Espania yan mulkin mallaka sun janye daga kasar Sahrawi Democratic Republic. Turawan Espani sun mamaye kasar Sahrawi ne tun shekara ta 1884. Sai dai tun lokacinne kuma mutanen kasar suka kafa rundunar gwagwarmaya da turawan mai suna Polisario. Sai bayan gwagwarmaya na shekaru turawan sun amince da bawa kasar 'yanci, sai dai bayan ficewars kasashen Morocco da Mauritania sun bukaci a raba kasar a tsakaninsu. Kashe 2/3 na kasar Morocco sannan 1/3 na Mauritani. Don haka ne mutanen kungiyar Polisaria suke fafatawa da gwamnatin kasar Morocco tun lokacin sannan har yanzun ba'a warware wannan matsalarba.