Dec 13, 2016 15:34 UTC

Yau Jumma'a 26-Aazar-1395H.Sh= 16-R-Awwal-1438H.K.=16-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  1437  da suka gabata a rana irin ta yau wato  16-R-Awwal-Shekara ta Farko bayan hijira. Bisa wasu ruwayoyi Manzon All..(s) ya gabatar da sallar jumma'a ta farko a musulunci. Kafin haka manzon Al…(s) ya yi hijira daga makka zuwa madina a ranar daya ga watan R-Awwal, sannan bayan isarsa madina kusa da wani kauye da ake kira quba, ya sauka a unguwar Bani Salam , a nan ne kuma jumma'a ta farko da riske shi, don haka ya gabatar da sallar jumma'a ta farko, bayan bada ta farko da ya samu a unguwar ya kuma fara da gabatar da khudubobi biyu gajeru kafin ya bada sallar jumma'a mai raka'oi biyu. A halin yanzu dai masallacin da aka fara sallar jumma'a a cikinsa yana nan tsake a wannan wurin ga wanda yake bukatar ziyarar gidan ido da kuma neman albarkansa.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Decemban-1950M. Mutanen kasar Cyprus sun fara gwagwarmayan kwatar 'yencin kasar daga hannun turawan ingila yan mulkin mallaka. Kafin haka dai kasar Cyprus mai fadin kasa kilomita murabba ee 9,251 tana karkashin ikon daular Usmania ne tun karni na 16 miladiyya, sannan a lokacinda Daular usmania ta shiga yaki da kasar Rasha a shekara ta 1877 sai tare da izinin turkawan turawan ingila ta shiga yankin tsibirin Cyprus a cekin tekun medeteranin daon taimaka mata. Wannan halin ya ci gaba har bayan yakin, har kuma zuwa farkon yakin duniya na daya inda daular Usmaniya ta shiga bangaren kasar Jamus a yakin, don haka ne turawan ingilan suka kwace iko da tsibirin na Cyprus. Bayan yakin duniya na biyu kuma bayan faduwar daular usmania mutanen Cyprus suka sami 'yencinsu daga hannun turawan a shekara 1960. Sai bayan haka kasar Turkia ta mamaye arewacin kasar ta Cyprus da sunan kare tsirarun kabilar turkawa mazauna tsibirin a shekara ta 1974.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa Shewa shekaru 18 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Decemban-1998M. Wata kotun daukaka kara a birnin Paris na kasar Faransa ta tabbatar da hukuncin dauri kan Proff. Roger Garaudy, wani dan siyasar kasar ta Faransa wanda kuma ya musulunta, kan laifin rashin amincewa da kisan kiyashin da ake riya cewa an yiwa yahudawa a kasar Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.

Proff. Roger Garaudy ya kawo kwakwaran dililai a cikin littafinsa masi suna –Tatsuniyoyin ginshigan saiyasar Israela- inda ya karyada faruwan abinda yahudawan sahyonia suke kiran holocos, ya kuma bayyana cewa yahudawan suna aiki tare da jamusawa ma a lokacin yakin, kuma sun kirkiro tatsuniyar cewa an kasha yahudawa miliyon 6 a yakin duniya na biyu a kasar Jamus ne kawai don bukatar kasashen duniya su tausayawa masu su kuma taimaka masu wajen kafa kasar HKI a kan kasar Palasdinu.

Wannan hukuncin dai ya nuna cewa kasar Faransa wacce ta shahara da sunan mashinfidan democradia na farko  a duniya ba gaskiya bana, don duk wanda ya rubuta ko ya fadi abinda ya sabawa yahudawa ba zasu kyaleshi ba.