Dec 13, 2016 15:37 UTC

Yau Asabar 27-Aazar-1395H.Sh= 17-R-Awwal-1438H.K.=17-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1491   da suka gabata a rana irin ta yau wato  17-R-Awwal-53 Kafin hijira, ko kuma shekarar giwaye. Aka haifi fiyeyyen halittu manzon All..na karshe ga bil'adama a birnin Makka. Sunan mahaifinsa Shi ne Abdullahi dan Abdulmuttalib, sannan sunan mahaifiyarsa Aminatu bint Wahab. Mahaifinsa ya rasu kafin haihuwarsa, sannan yana dan shekara 6 a duniya ya rasa mahaifinsa. Manzon All.. ya fara karban wahatin Al-qur'ani mai girma yana dan shekara 40 a duniya, sannan bayan shekaru 13 da kira zuwa ga musulunci a Makka ya yi hijira zuwa madani, inda ya kafa daular musulunci ta farko, sai kuma shekaru goma bayan haka, ya rasu yana dan shekara 63 a duniya. Kafin rasuwarsa dai addinin musulunci ya mamaye mafi yawan kasashen larabawa. Banda haka bayan rasuwarsa da kadan addinin musulunci ya kada manya manyan daulolin duniya na lokacin ya zama addini da kuma daula mafi girma a duniya. Muna taya al-uammar musulmi da ma dukkan bil'adama da wannan babban rana ta haihuwar manzon Al..(s).

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1355 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-R-Awwal-83H.K. Aka haifi limami na 6 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) a garin Madina. Imam Jaafar bin Mohammad (a) wanda ake wa Lakabi na Sadiq ya gudanar da farkon rayuwarsa a gaban mahaifinsa Imam Mohammad bin Ali (a) sannan bayan shahadar mahaifinsa a shekara ta 148 ragamar jagorancin al-ummar kakansa ya koma wuyarsa. Imam Sadiq (a) ya shara da yawan ilminsa, banda haka kuma hattama limaman mazhabobin sunnan guda hudu sun amfana da ilminsa ko kai tsaye, kamar Imam Abu hanisa, numan bin thabit, wanda ya share shekaru 2 yana karatun a gaban imam Sadiq (s) harma an ruwaito shi yana cewa –fa laua sanatani la halakan Annuman. Inda yake ishara da shekaru biyu da ya dauki karatu a gabansa. Sai kuma sauran liman duk sun fa'idantu da ilminsa ta hanyar dalibansa. An ruwaito cewa manya manyan malamai a birni Kufa na kasar Iraqi kimabi 4000, ko wannensu yana cewa ya ruwaiti hadisi daga Imam Sadik (a). Muna taya al-ummar musulmi musamman mabiya mazahabar Jaafaria murnar ranar haihuwarsa.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 170 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-R-awwal-1268H.K. An kasha Amir Kabir sadrul azzam wani babban dan siyasa kuma priministan gwamnatin sarki Nasiruddeen Qajar. Amir Kabir ya kasance mutum ne mai maiki tukuri wa al-umar Iran a lokacin ya kuma yi aiki da sarakunan kajarawa da dama. Har ma ya kai ga sarki nasirudden kajar ya aurara masa diyarsa guda don kusancin da suke da shi. Amma bayan wani lokaci masu hasada suka shiga tsakanin musamman ganin yana hana turawan shiga cikin harkokin mulkin kasar Iran, suka hada shi da sarki wanda ya tube shi daga mukaminsa, sannan daga baya ya bada umurnin kasha kasha. Bayan kutuwarsa an kai gawar Amit kabir kasar karbala na kasar Iraqi inda aka bisne shi a haramin Imam Husain (a).