Ko Kun San na (274) 28 Aazar Shekara ta 1395 Hijira Shamsia
Yau Lahadi 28-Aazar-1395H.Sh= 18-R-Awwal-1438H.K.=18-Decemba-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1437 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-R-Awwal-Shekara ta farko bayan hijira. Aka fara gina masallacin manzon Al…(s) da ke Madina. Bayan hijirarsa daga makka zuwa Madina abu na farko wanda manzon Al…(s) ya fara yi shi ne gina masallacinsa. An gina masallacin ne da duwatsu da tubali da kuma katako da ganyen dabino, kuma manzon Al..(s) da kansa ya shiga cikin aikin. Masallacin Madina dai shi ne masallashi mafi daraja bayan masallacin da ke kewaye da dakin Kaaba. Kuma manzon All..(s) yakan amfani da shi don ibada, karantarwa wa'azi shawara da kuma warware matsalolin musulmi da kuma hukunci a tsakaninsu. A halin yanzu dai miliyoyin musulmi daga dukkan fadin duniya ne suke ziyartar masallacin da kuma kabarinsa da ke cikinsa.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Decemba-1979M. Babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince da wani kuduri wanda ya bukaci dauke dukkan shingen da suka hana daidaito tsakani mata da maza a duniya. Wanan kudurin dai yana da maddoji 30 wanda ya bukaci daidaita mata da maza a dukkan bangarorin rayuwa. Sai dai kamar yadda muka saba, ra'ayin kasashen yamma shi ne a gaba wajen samar da wannan kudurin don haka sun tsari saha ba tare da lura da yaniyan halittan mace da kuma abinda ya dace da halittar taba, shi ya sa mafi yawan addinan sama musamman addinin musulunci yana ganin mace don irin yanayin halattanta da ruhinta akwai ayyuka da kuma matsayin da suka dace da ita wani lokacimma ya kebanceta, don haka dole ne a lura da wannan a duk lokacinda ake baganar hakkin mata. Da wannan dalilin ne ma zaka gana an dau shekaru da samar da wannan kudurin amma ba wani sauyi a cikin rayuwar mace musamman macce da ke rayuwa a kasashen yamma.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 26 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Azaar-1369H.SH. Sadiq Ganji jami'a mai kula da bangaren al-adu na ofishin jakadancin Jumhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Lahor na kasar Paksitan ya yi shahada a hannun yayan wata kungiyar yan ta'adda masu saman goyon bayan kasashen yamma.
Shekaru 4 cur Sadiq Ganji yana aiki a wannan bangare a kasar Pakistan, amma bayan kammala aikinsa yana kan hanyarsa ta komawa gida Iran sai ya halarci wani taro na girmamashi a birnin Lahor na kasar Pakistan inda ya yi bankwana da mutane a taron amma kafin ya koma gida wani dan ta'adda ya bindigeshi wanda sanadiyyar haka ya kai ga shahada.