Jan 07, 2017 04:32 UTC

Yau Litinin 29-Aazar-1395H.Sh= 19-R-Awwal-1438H.K.=19-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  229  da suka gabata a rana irin ta yau wato  19-Decemba-1787M. Kasar Salio dake yammacin Afrika ta koma karkashin mulkin mallakar turawan Ingila yan mulkin mallaka bayan shekaru 327 na mulkin mallakar turawan Potigal. Turawan Potigar sun shiga kasar Salio ne tun karshen karni 15 miladiya, wato a shekara 1460M. kuma tun lokacin ne suka fara shimfida ikonsu a kasar, banda haka sun maida kasar Salio a matsayin kasuwar bayi ta duniya a yammacin Afrika, a dan tsakanin wadan nan shekaru, turawan na Potigal sun said dubban daruruwan bakaken fata maza da mata ga kasashen Turai da Amurka.

Sai dai bayan da turawan Ingila suka sami nasarar korar turawan Potigal daga kasar ta Salio a shekara 1787M, wannan halin bai sauya ba. Turawan ingila sun ci gaba da yiwa mutanen kasar salio Mulkin mallaka da kuma saida su a matsayin bayi har zuwa shekara 1961M, a lokacinda ta suka bawa mutanen kasar cin gashin kai, sai kuma a shekara 1971 kasar Salio ta zama jumhuriya. Kasar Salio dai tana da fadin kasa kilomita murabbaee 71,740.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 164 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Decemba-1852M.  Aka haifi Albert Abraham Michelson  wani fitaccen masanin ilmin kimiyyar lissafi dan kasar Amurka a Amurkan. Michelson ya fadada ayyukansa ne a bangaren gwaje gwajen haske, kuma ya sami nasarori da dama a wannan bangaren. Daga cikin nasarorin da Michelson  ya samu a wannan bangaren sun hada da samar da wata na'ura wacce ake kira Interferometer wacce take gwada saurin haske. Banda haka Michelson ya gano wasu dokoki da suka shafi haske, wadanda kuma suka suke bude kofofin sabbin fahinda da kuma ci gaba da bincike a bangaren. Albert Abraham Michelson ya karbi kyautar Nobel a shekara 1907M don irin nasarori da kuma ci gaban da ya samar a wannan fannin.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 96 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Decemban-1299H.SH. Mulla Fathullahi Garawi Esfahani daya daga cikin manya manyan amalaman addini a nan kasar Iran ya rasu. An haife Mulla Esfahani a birnin Esfahan a na Iran. Ya kuma fara karatu a gida, sannan ya je birnin Mashad inda ya fadada ilminsa a gaban manya manyan malamai na lokacin. Sai kuma daga baya ya kammala karatunsa a birnin Najf na kasar ta Iranqi. Bayan haka ne ya bude ajujuwan karatu ya fara karantarwa da kuma wallafe wallafe. Mulla Esfahani ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai

 «قاعده لا ضرر»، «قاعده طهارت»    da kuma «افاضة التقدیر فی احکام العصیر». Har ila yau Mullah Fathullah Garawa Esfahani yana daga cikin malaman addinin da suka fito don yakar turawan Ingila wadanda fara mamayar kasar Iraqi a lokacin, duk da cewa turawan sun fi karfinsu daga baya.