Ko Kun San na (276) 30 Aazar Shekara ta 1395 Hijira Shamsia
Yau Talata 30-Aazar-1395H.Sh= 20-R-Awwal-1438H.K.=20-Decemba-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 30 ga watan Azaar na wannan shekara ta 1395 hijira shamsia, daren irin ta yau ce a ko wace shekara ta fi tsawo, inda rana takan fadi 5.15 sannan gari ya wayi da misalin 6 saura 20. a nan Iran, amma a wasu yankuna a kasashen arewacin kasar Rasha da wasu kasashen Turai daren na tsawon sa'oi 24. a nan Iran dai sukan kira daren da daren Yalda. Kuma a yincin da yake biyo daren ne ake yini mafi gajerta. Banda haka daren yolda tana bayyana shigar fasali na zubar dusar kankara na tsawon wattannin ukku, don haka masu noma sun kan yi farinciki da shigar wannan fasali don bayansa ne suke amfana da ruwan da zubar kankarar take samarwa don ayyukan noma. Raya wannan daren dai al-adace ta Iraniyawa da wasu kabilu a yankin tun kaka da kakannin.
03-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 81 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-decemba-1935M. Sheikh Izzuddeen Qassam shugaban Palasdinawa masu gwagwarmaya da mamayar kasar Palasdinawa ya yi shahada. Kafin haka dai izzuddeen Qassam ya kammala karatun jami'a ne a jami'am al-azhar a birnin Al-kahira a gaban manya manyan malamai na lokacin wadanda suka hada da sheikh Muhammad Abdu shugaban Jami'ar a lokacin. Bayan kammala karatu da dawowarsa gida Palasdinu Sheikh Al-qassam ya ga turawan ingila yan mulkin mallaka suna taimakawa yahudawan sahyoyinia wadanda suke kwarara daga kasashen turai zuwa kasar Palasdinu da sunan kafa HKI. Wannad ya sa sheikh al-qassam ya dauki makama don yakin turawan a shekara ta 1930. Amma bayan share kimani shekaru 5 yana gwagwamaya da su a rana irin ta yau a wani harin da aka kai masa a gidansa yahudawan sun kasha shi sun kuma kaishi ga shahada.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Aazaar-1364H.Sh. Gwamnatin kasar Tarayyar Soviet ta lokacin ta rattaba hannu kan yerjejeniyar sayarwa gwamnatin kasar Iraqi makamai masu yawa. Wannan yerjejeniyar ta zo ne a dai dai lokacinda ake ci gaba da fafatawa tsakanin sojojin kasar Iraqi wadanda suke mamaye da wasu yankunan kasar Iran da sojojin kasar Iran. Tarayyar Soviet dai tana kokarin shimfida ikonta a wasu kasashen yankin ne bayan da ta rasa abinda take samu a kasar Iran bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara ta 1979. Yawan makaman da tarayyar Soviet ta sayarwa sadam husai na kasar Iraqi a lokacin dai ya kai kaso 60% na makaman da kasar take bukata. Sai dai duk tare da wannan taimakon a karshen yakin Iraniyawa ne suka sami nasara kan Iraqi.