Jan 07, 2017 04:36 UTC

Yau Laraba 01-Day-1395H.Sh= 21-R-Awwal-1438H.K.=21-Decemba-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 195 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-R-Awwal-1243H.K. Birnin Irawan daga daga cikin manya manyan birane karkashun sarakunan dangen Kajarawa ya fice daga ikon daular Iran da ta lokacin ya kuma koma karkashin daular Rasha. Kafin haka dai sojojin kasashen biyu sun yi ta fafatawa kan mallaka birnin, sai daga daga a karshe a rana irin ta yau sojojin Rasha sun sami nasara a kan sojojin Sarki Ali-Fat Kajar sun kuma kwace birnin. Bayan haka ne aka kulla wata yerjejeniya tsakanin daulolin biyu, yerjejeniya wacce ake kira Turkemon-Chai. Inda a cikinta daular kajarawa don tsananin raunit ta rasa wasu yankunan da dama arewacin Ajarbajan da kuma Qafqas.

02-Masu sauraro ko kun cewa shekaru 192 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Decemba-1824M. Jeams Pakinson wani likita dan kasar Brirania, wanda ya gano cutar Pakinson ya rasu yana dan shekara 69 a duniya. Pakinson ya koyi aikin likitanci a gaban mahaifinsa ya kuma kore a kai. Jeams Pakinson ya gudanar da bincike kan wasu cututtuka da dama wadanda suka hada da cutar kumburin babbar yatsar kafa da ake kira Gout da kuma cutar makerketa wacce ake Pakinson. A shekara ta 1805 ya rubuta wani karamin littfi dangane da cutar da Gout. Sannan a shekara ta 1912M ya gano cewa cutar da ake kira Apendix tana iya kashewa a shekara ta 1812. Bayan haka ne kuma ya gano musabbin cutar makerketa ta pakinson a shekara ta 1817. Cutar Pakinson dai cutar ce ta kwakwalwa, wacce take sanya tafiya a hankila sannan take jawo makerkertan jiki a dai dai lokacinda mutum yake zaune, kuma tana aukuwa ne ga tsoffi a mafi yawan lokuta.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Decemba-1988M. Wani jirgin fasinja mallakin kasar Amurka ta fada a kan kauyen lokabi a cikin yankin scortlanda na kasar Britania ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane 270 da suke cikinsa, mafi yawansu Amurkawa. Bayan yan kwanaki da hatsarin ne kasashen Amurka da Britani suka zargi mutanen biyu yan kasar Libya da dana boma boman. Suka kuma tilastawa majalisar dinkin duniya dorawa kasar Libya talunlumai daban daban wadanda suka hada da hanata saida danyen man fetur, hana tashin jiragen sama a kasar da sauransu. Wannan halin ya kuntatawa kasar Libya har ta abince da mika mutanen a shekara ta 1999. Sanna bayan an gurfanar da su an salami guda an kuma daure guda na tsawon rai da rai. Sannan aka tilastawa Libya biyan diyyar duk wadanda suka rasa rayukansu a jirgin, sannan ne aka dage mata takunkuman.