Mar 07, 2016 14:49 UTC

Yau Talats 25 –Esfan-1394 H.Sh=05-Jamada-Thani -1437H.K.=15-Maris-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 790 da suka gabata a rana irin ta yau wato  5-Jamada-Thani-647 H.K. Aka haifi Allamah Hassan bin Ali bin Dawuda Halli a garin Hilla na kasar Iraqi. Allamah Hilli ya fara karatu garin na Hilla wanda ya kasance cibiyar karatu a lokacin. Allamh Hilli ya kamala karatunsa a gaban manya manyana malamai na lokacin wadanda suka hada da Sayyeed  Ibn Tawoos da kuma Muhakkiq Hilli. Bayan haka Allamah Hillli ya fara karantarwa da kuma wallafe wallafe. Cikin littafan da ya rabuta akwai «الرجال» kan ilmin hadisi da masu ruwaitosu. Sai kuma اُرجوزة فی الکلام»، «تحصیل المنافع» و «جواهر الکلام فی الاشباه و النظائر» Allah Hassan bin Ali bin Dawuda Hilli ya rasu a shekara ta 707H.K.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 765 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Jamada-Thani-672H.K. Maulana Jalaluddeen Mohammad Balkhi wanda aka fi saninsa da Maulawi ya rasu a wani gari da ake kira Khooniyeh a kasar Turkia. An haifi maulawi a shekara ta 604 a garin Balkh dake cikin kasar Afganistan a halin yanzu. Maulawi shi ne malamin addini wanda ya fi shahara da iya wakokin a cikin karni 7 hijira kamaria. Maulawi ya hada da wani malamin arfani mai suna Shamsu Tabrizi wanda ya sauya masa tunani. Sai kuma daga nan ya bar karatu ya koma tarbiyan naf. Daga karshe ya rubuta littafai da dama wadanda suka hada da  «مثنوی معنوی» .«فیهِ ما فیه»، «مکتوبات مولانا» و «رباعیات».


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Esfand-1366H.SH. Jaragen yaki da kasar Iraqi a lokacin mulkin Sadam Husain sannan a dai dai lokacinda take yakar kasar Iran sun cilla makaman guba a kan Qurdawa mutanen garin Halabja inda makaman suka kasha mutane da dama. Sadam Husain ya dauki fansa ne kan muatnen garin Halibja bayan karban mutanen iran da suka yi. Kasashen yamma wadanda suke tallafawa sadam Husain da sinadaran hada wadan nan makamai sun gum da bakunansu kan wannan ta’asar.

Tags