Mar 07, 2016 14:57 UTC

Yau Laraba 26 –Esfan-1394 H.Sh=06-Jamada-Thani -1437H.K.=16-Maris-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 39 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Maris- 1977M . Kamal Jumbulad wani dan siyasa a kasar Lebenon yam utu a hannun abokan hamayyarsa. An haifi Kamal Jumblad a ranar 6-Satumban-1917M. a kudancin birnin Beyroot. Jambulad ya shiga harkokin siyasa a shekara ta 1952 M. Wani abu mai muhimmanci a rayuwar Jamblot shi ne yana daga cikin wadanda suke goyon bayan Palasdinawa a kan gwagwarmayan da suke yi da HKI musamman a yakin shekara ta 1967M. Bayan haka yana matukarr adawa da shigar sojojin kasar siria a kasar Lebanon. Amma bayan da gwamnmatin kasar ta amince da hakan ya zama bai da wata mafita , don haka shi ma ya amince da hakan amma har zuwa ranar da aka kasha shi yana adawa da kasantuwar sojojin siria a cikin kasar Lebanon. An kashe Kamal Jumblad yana dan shekara 60 a duniya.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 21 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Esfand-1373H.SH. Sayyeed Ahmad Khomaini dan Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya rasu shekaru shidda bayan rasuwar mahaifinsa. An hafi Sayyeed Ahmad a shekara ta 1324 H.SH a garin Qum, kuma ya tashi a gaban mahaifinsa Imam Khomaini (q) inda ya sami tarbia na gwagwarmaya da azzaluman sarakunan Iran. Sayyeed Ahmad ne yake kai kawo tsakanin mutanen kasar Iran da Mahaifinsa Imam Khomaini (q) a lokacinda yake gudun hijira a kasashen waje. Sanna bayan samun nasara ma ya kasance tare da mahaifinnsa duk tare da cewa an bukace shi da ya rike mukamai masu muhimmanci a kasar. Sayyeed Ahmad ya bayyana goyon bayansa ga Imam Aya. Sayyed Aliyul Khamania bayan zabensa da majalisar khubrigan suka yi.


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 2 da suka gabata a rana irin ta yaua wato 16-Maris-2014M. Mutanen yankin Cremia na kasar Ukrai sun zabe hadewa da kasar tarayyar Rasha. Kafin haka dai bayan faduwar gwamnatin shugaba Victo Yunkovic na kasar Ukrai, sojojin rasha da suke tekun Black sea sun mamaye yankin Cremia sannan daga baya sojojin rasha suka shiga yankin. Sai kuma don halattawa kanta mamayar yankin gwamnatin kasar Rasha ta gudanar da zaben jin ra’ayi mutanen yankin Cremia inda suka zabi hadewa da tarayyar rasha a rana irin ta yau. Mafi yawan muatnen yankin Cremia dai yan kabilar Rasha ne.


Tags