Ko Kun San Na (44) 13 Urdeebehesht Shekara Ta 1396 Hijira Shamsia
Yau Laraba 13-Urdeebehesht-1396H.SH=06-Shaaban-1438H.K.=03-Mayu-2017M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 163 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13 –Urdeebehesht-1233H.Sh. Mirza Habibullahi Shirazee , wani kwararren mai tsara wakoki masu hikima ya rasu. An haifi Mirza shirazi a shekara ta 1187 H.Sh a kudancin kasar Iran. Mirza shirazi ya fara karatu ya kuma kammala a cikin shekaru 10 a birnin Mashad na kasar. Tun lokacin ne kuma ya fara rera rubutattun wakoki wadanda yake rubutawa da kansa.
Kafin rasuwar a shekara ta 1233H.SH yana dan shekara 47 a duniya Mirza Shirazi ya bar mana diwanin wakokinsa wadanda suka kai baituka dubu 18 a cikin harsuna farinsanci da Larabci.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 88 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Shaaban-1350H.K. Mirza Lutfu-Ali malami masanin ilmin adabin larabci ya rasu a nan Iran. An haifi Lutfu-Ali a birnin Tabriz a nan ya kuma tashi a nan Teran a gaban mahaifinsa inda ya fara karatu ya kuma kammala a nan. Mirza Lut-Ali bin Mohammad Kazin Tabrizi ya fara tsara wakoki tun yana yaro, sannan bayan kammala karatu a fara karantarwa da kuma wallafa littafai. Littafi «فانى» na daga cikin littafan da Lutuf-Ali ya bar mana, a lokacin rasuwarsa a shekara ta 1350 H.SH yana dan shekara 82 a duniya.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 24 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Mayu-1993M. Bisa sahawarar hukumar Unesco mai kula ta harkokin ilmi da al-adu ta MDD , majalisar ta sanya ranar 3 ga watan mayu na ko wace shekara ta zama ranar kafafen yada labarai da marubuta. Kafafen yada labarai dai sun hada da radio, jaridu, tashoshin television da sauransu. Manufar ware wannan ranar ita ce tunatar da duniya hakkokin yan jarida da kuma kafafen yada labarai da kuma marubuta, musamma a kasashen da shuwagabanninsu suke takuwarwa yan jarida don suna daukarsu a matsayin barazana a garusu.
Sai dai a wani bangare kuma musamman a kasashen yamma an dauki 'yencin fadin albarkacin baki nay an jaridu wata dama ta cin mutuncin mutane da al-umma, wani lokacimma har tare da wulakanta addinan All.. da suna 'yencin fadin albarkacin baki.