Jun 19, 2017 04:02 UTC

Yau Alhamis 14-Urdeebehesht-1396H.SH=07-Shaaban-1438H.K.=04-Mayu-2017M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru  72 da suka gabata a rana irin ta yau wato 4-Mayu-1945M.  Aka wargaza jam'iyyar NAZI ta kasar Jamus bayan yakin duniya na biyu. An kafa jam'iyyar Nazi ce a shekara ta 1932, kuma bayan ta sami iko da kasar Jamus a shekara ta 1939 ta fara yakin duniya na biyu karkashin jagorancin Adolf Hitala. Manufofin Jam'iyyar Nazi dai sun hada da karfafa kabilar jamusawa da kuma harshenta a duniya. Har'ila yau da nuna fifikon jamusawa a kan sauran Kabili. Amma bayan shekaru 13 da kafata a rana irin ta yau an wargaza jam'iyyar har abada. Sai dai duk tare da wargaza jam'iyyar a halin yanzu akwai wasu jamusawa da suke kokarin sake tada ikidun wannan jam'iyyar , har ma wasu daga cikinsu sun sami damar shiga majalisun dokokin kasashen Jamus da Italia.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 04-Mayu-1980M. Tsohon shugaban kasar Ugoslavia Marshal Josept Titu ya rasu. An haifi Titu a kasar kasar Yugo salavia a kafin yakin duniya na daya. Sannan yana daga cikin sojojin kasar da suka yi yaki a yakin duniya na daya. A yakin duniya na biyu kuma rundunarsa mai mayaka dubu na biyu ta kare kasar Ugosalavia daga fadawa karkashin kasar sojojin Hitla na kasar Jamus. Bayan haka me a shekara aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Ugoslavia a shekara 1953. Sannan a shekara ta 1974 aka tabbatar masa shugabancin kasar na tsawon rayuwarsa.

Titu dai yana daga cikin shuwagabannin duniya da suka kafa kungiyar yan ba ruwammu ta Non Alliance movement . Titu ya rasu a rana irin ta yau bayan fama da cuta na lokaci mai tsawo.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Urdeebehesht-1360H.SH.  Wani jirgin yakin kasar Iraqi a dai dai lokacinta take cikin yakin shekaru 8 da Iran ya kakkabo jirbin saman ministan harkokin wajen kasar Algeria a sararin samaniyar JMI bayan wani ziyarar aiki wanda ya kawo nan Tehran. Bayan faduwar jirgin dai JMI ta aike da tawaga ta musamman karkashin jagorancin wani babban jami'an gwamnati wanda ya tabbatar da cewa jirgin yakin  kasar Iraqi ce ta kakkabo jirgin saman ministan harkokin wajen na kasar Algeria Bin Yahyah.

Bayan wannan mummunan ta'asadr dai kaashen larabwa da kuma sauran duniya sun gano hakikan yadda shuwagabannin kasar Iraqi suke.