Jun 19, 2017 04:04 UTC

Yau Jumma'a 15-Urdeebehesht-1396H.SH=08-Shaaban-1438H.K.=05-Mayu-2017M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1132 da suka gabata a rana irin ta yau wato 08-Shaaban-306H.K. Aka haife Sheikh Assuduq babban malami a mazhabar shia a birnin Qum na kasar Iran. Abu Jaafar bin Aliyu bin babawai ya fara karatu tun yana karami a gaban mahaifinsa. Bayan ya isa wani matsayi na ilmi ya fara zagaya kasashen musulmi don tattara hadisan manzon All…(s) da iyalan gudansa. Sheikh Saduk ya karbi hadisai a gaban malamai fiye da 200, sannan makaransa da ya bude a Bagdaza ta tattara manya manyan malamai na zamanin wadanda suka hada sheikh Almufeed, Hassan bin Muhammad Qumi, Alamul Huda sayyeed Murtada da sauransu. Sheikh Sudu ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai

"من لایحضر الفقیه" cikin mujalladai 4 , kuma wanda yake dauke da hadisai dubu 6 kuma yake cikin manya manyan littafai hudu na hadisi wanda malaman shia suke dokaga da su. Sanna akwai مدینه العلم , cikin mujalladai 10, امالی، خِصال، عیون اخبار الرّضا(ع) و عِلَلُ الشرایع.

Sheikh Saduk ya rasu a garin Rai nan kusa da birnin Tehran a shekara ta 380 yana dan shekara 75 a duniya.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 877 da suka gabata a rana irin ta yau wato 8-shaaban-561H.K. Aka haifi Ibn Rumi wani babban malamin hadisi kuma masanin ilmin magunguna a kasar Andulus na kasar Espania a halin yanzu. Ibn Rumi ya tashi da karutu a gida, kuma yana matashi ya zama babban malami a zamaninsa. Bayan haka ya ziyarci wasu kasashen musulmi wadanda suka hada da Masar Hijazz da kuma Iraqi. Ibn rumi ya rubuta littafai da dama sai dai wasu faga cikinsu sun bace.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 73 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Urdeebehesht- 1323H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya gabatar da jawabinsa na farko kan gwagwarmaya da azzaluman shuwagabannin musamman na Iran don kare addinin musulunci da kuma mutuncin musulmi. A cikin bayanin nasa dai, Imam ya nuna cewa hanyar gwagwarmaya da azzaluman shuwagabannin kasashen duniya ne kawai mafita daga halin da musulmi da addinin musulunci suka shiga kuma tafarkin ne tafarkin annabawa da manzanni. Imam ya nuna irin nauyi mai yawa da ya rataya a kan malaman addinin wajen farkar da al-umma kan halin da rake ciki. Tun bayan wannan jawabin ne imam ya fara samun mabiya wadanda da su ne ya kafa gwagwarmayansa na kauda zalunci a kasar Iran. Imam yana dan shekara 42 a duniya ne ya gabatar da wannan jawabin mai muhimmanci.