Ko Kun San Na (47) 16 Urdeebehesht Shekara Ta 1396 Hijira Shamsia
Yau Asabar 16-Urdeebehesht-1396H.SH=09-Shaaban-1438H.K.=06-Mayu-2017M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 957 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Shaaban-481H.K. Ibn Barraja fitaccen malamin fikihu na kasar Masar ya rasu. An haife Ibn Barraj a kasar Masar, amma bayan kammala karatu na yi aikin alkalanci a birnin Tarabulus ko Tripoli na arewacin kasar Lebanon don haka ne aka fi saninsa da Tarabulusu. Ibn Barraja ya yi karatu a gaban manya manyan malaman shia a kasar Lebanon a lokacin, wadanda suka hada da Sayyeed Mutada da kuma Sheikh Toosi.
Malamin ya yi zurfi a ilmin fikihu ta yadda manya manyan malamai suna komawa da littafansa don neman ilminsa. Kuma yana da littafi mai suna «الجوامع الفقیه» inda ya amsa tambayoyin fikihu 820.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 135 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Mayu-1882H.SH. Proffeser Robert Koch wani likita dan kasar Jamusa ya gano kwayar cuta wacce take haddasa cutar Tarin Tb. Kafin haka dai cutar Tab ta kashe fiye da mutane biliyon daya a duniya. Kuma bayansa da kadanne aka samar da maganin cutar ta Tab.
Bandaa haka Robert Koch ya ne gane kwayar cutar annobar cholera bayan wani bincike da ya gudanar a kasar Indai. Hakanan shi ne ya samar da maganin malaria mai suna Atox wanda yake kama da Quinin.
An haifi Kocn a ranar 11-Decemban-1843- sannan ya rasu a ranar 27-Mayu-1910shekara ta. Kafin rasuwarsa da shekara guda wato a shekara 1905 karbi kyautar Nobel ta ilmi.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Urdeebehesht. Aya. Ruhullah Kamalvand daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan Iran ya rasu a garin Khuramabad. An haife shi a shekara ta 1330 a garin Khuramabad sannan ya kammala karatunsa na addini a hauza ilmiyya ta Qum a nan Tsakiyar kasar Iran. Aya. Kamalvand ya yi karatu tare da Aya. Khomaini (q) wanda ya assada JMI da kuma Aya, Galpaya gani. Sanna yana dan shekara 50 a duniya ya koma gida Khuramabad inda ya zama jagora mai tasiri a cikin al-ummar khuramabad.