Mar 05, 2018 08:19 UTC

Yau Jumma'a 25-Esfand-1396H.Sh=27-J-Thani-1439H.K=16-Maris-2018M

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1323  da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-J-Thani-116H.K. Aliyu Bin Muhammad dan Imam Mohammad Bakir(a) limami na 5 daga cikin limamai masu tsarki ya yi shahada. Kafin haka dai Imam Bakir(a) ya tura dansa Aliyu zuwa garin Kashan a nan Iran inda yake yada ilmin kakansa ga mutanen yankin. Kafin shahadarsa Aliyu bin Muhammad ya rubutawa mahaifinsa wasika inda yake bayyana masa irin halin da shi da mabiyansu suke a garin na Kashan. Amma ba'a dade ba makiya suka farmasu ya yaki. Aliyu bin Muhammad bayan shekaru 3 da aikin isar da sakon musulunci a garin Kashan, tare da magoya bayansa kimani 100 sun fuskanci makiya a wani wuri da ake kira" Mashade Urdehol" sun yi shahada kamar yadda kakansa Imam Husain (a) yayi a katbala. A halin yanzu akwai hubbarensa inda masoya iyalan gidan manzon Allah suke ziyartarsa a duk tsawon shekara.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 30 da suka gabata  arana irin ta yau wato 25-Esfand-1366H.Sh. Gwamnatin kasar Iraqi ta lokacin karkashin shugabancin Sadam Husain ta yi ruwan boma-boman makaman guba a kan mutanen Halabja na Kasar ta Iraqi da ke arewa maso gabacin kasar. Wannan harin ya auku ne a dai dai lokacinda sojojin sadam suke samun koma baya a yakin da suke yi da JMI da kuma tare da kurdawan kasar wadanda suma suka gaji da zaluncinsa suke kuma taimakawa Iraniyawa a wannan yakin. Mutane kimani 5000 suka rasa rayukansu sanadiyyar shaker iska mai guba a wannan harin sannan wasu da dama suka ji rauni. Amma kasashen yamma wadanda suka bawa sadam Husain fasahar kire makaman sun gum da bakunansu kamar ba abinda ya faru.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 4 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Maris-2014M. Mutanen yankin Cremia na kasar Ukrain sun zabi hadewa da jumhuriyar Rasha a wani zaben raba gardamar da gwamnatin Rasha ta gudanar a yankin. Kafin haka dai bayan faduwar gwamnatin Victo Yonkovich a kasar Ukrai rikici ya tashi tsakanin sabuwar gwamnatin kasar da kasar Rasha, wanda ya sanya sojojin Rasha suka mamaye yankin Cremia. Sannan ta gudanar da zaben raba gardama a yankin don halattawa kanta hadewar yankin da tarayyar Rasha. Mafi yawan mazauna yankin Cremia dai yan kabilar Rasha ne.

 

Tags