Mar 05, 2018 08:21 UTC

Yau Asabar 26-Esfand-1396H.Sh=28-J-Thani-1439H.K=17-Maris-2018M

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1382  da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Maris-636M. Musulmi a karon farko sun kwace iko da yankin Sham wanda ya hada da kasar Palasdinu da kuma Siria a halin yanzu. A lokacin Khalifa na biyu Umar bin Khaddab ne ya aike da sojoji don yakar rumawa wadanda suke  iko da yankin a lokacin. Wannan yankin ya ci gaba da zama karkashin ikon musul,I har zuwa shekara ta 1097 a lokacinda kiristoci daga kasashen turai suka fara yakin da ake kira yakin salibia. Sun kama kwace birnin Qudus da yankuna masu yawa a kasar Palasdinu. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara ta  1250M Salahiddeen Ayyuka sarkin kasar Masar na lokacin ya sake dawo da ikon musulmi a birnin. Sai kuma bayan yakin duniya na biyu turawan ingila sun mamaye Palasdinu sun kima mika ta ga yahudawan sahyoniyaa a shekara 1948, sannan yahudawa suka mamaye birnin Qudus a yakin shekara ta 1967. Har yanzun birnin Qudus na karkashin ikonsu.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 70 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Maris-1948M. Wakilan kasashen Ingila, Faransa, Beljika, Holand da Luxumburg sun kulla wata yerjejeniya a tsakaninsu ta taimakawa juna a bangarori tsaro da kuma tattalin arziki. An kulla yerjejeniyar Brusses ne a kasar Beljika, kuma bayan yan watannin wadannan kasashe sun gudanar da wani taro a kasar Amurka inda Amurka da Canada suka shiga yerjejeniyar suka kuma kafa kungiyar tsaro ta NATO. Wacce daga baya mafi yawan kasashen yammacin turai suka shiga.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san ncewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Esfand-1373H.Sh. Sayyid Ahmad Khomani dan marigayi Imam Khomaini(q) wanda ya assasa JMI ya rasu. An haifi Ahmad a shekarata 1324 H . Sh a birnin Qom. Ya Tashi a gaban mahaifinsa, inda ya sami tarbiyya da ilmin addini. Sayyid Ahmad ya kasance tare da mahaifinsa a lokacinda yake gudin hijira a kasashen Iraqi da Faransa kuma shi ne dan sakon imam zuwa mutanen Iran. Bayan nasara juyin juya halin Musulunci Sayyid Ahmad ya kasance kusa da mahaifinsa har zuwa rasuwasa a shekara 1368H.Sh . Sannan shi kuma ya rasu shekaru 6 bayan mahaifinsa. Ahmad yana goyon bayan Sayyid Aliyul Khaminae jagoran juyin juya halin musulunci na yanzu.

 

Tags