Najeriya : Shirin baiwa Matasa Dubu-biyar biyar (kashi na Biyu)
shirin a yau na zamen ci gaban wanda ya gabata ne wanda ya maida hankali kan matakin gwamnatin Najeriya na baiwa matasa naira dubu biyar-biyar a ko wanne wata
A bara ne dai gwamnatin Najeriya ta bakin ministan matasa da wasannin na kasar, Solomon Dalong ya sanar cewa jam’iyyar mai mulki zata bayar da tallafin Naira dubu biyar-biyar ga matasan kasar marasa ayyukan yi daga farkon shekara 2016, saidai a cikin wannan ne a wani abu da ake wa kyallon tayi amai ta lashe gwamntin ta ce sam ita batayi wannan alkawari ba, lamarin da ya tayar da zazzafar muhawara tsakanin matasan kasar.
Anyi amana cewar rashin aiki yi ga matasa a wannan kasa ya taimaka sosai wajen tursasawa matasan kasar aikata ayyukan da suka sabawa zamantakewar al’umma, irin su tada kayar baya da fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fasa bututu don satar man fetur da dangogin ayyukan ta`addanci da suka zama ruwan dare a wannan kasa.