Ko kunsan (21) Na 21 ga watan Farvaddeen shekara 1395 Hijira Shamsia.
Yau Asabar 21-Farvaddeen-1395 H.Sh=01-Rajab-1437H.K.=09-Afrilu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa yau ce daya ga watan rajab na wannan shekara? Wata wanda yace ciki da falala da albarka. Manzon Al.. (s) yana fada dangane da shi da kuma watanni biyu bayansa wato Shaaban da Ramadan cewa”(Watan Rajaba watan ne mai girma a wajen All.., babu wani wata wanda ya kai shi falala, an kuma haramta yaki da kafirai a cikinsa. Watan Rajab watan Al..ta’ala ne, watan Shaaban wata na ne, sannan watan Ramadan na al’ummata ce.)) . A cikin watan ne All.. ya zabi manzon Al..(s) da annabci. Har’ila yau a cikinsa ne aka haifi Amirul muminina (a). Ana kaidaitar da yawan azumi da wasu ayyukan alkhairi a cikinsa, don samun kusanci ga All...
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1380 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Rajaba-57H.K. Aka haifi limami na 5 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All…(s) wato Imam Mohammad Bakir dan Aliyu Zainul abideen (a) a madina. Bayan shahadai maifinsa a shekara 96 H.K. ya karbi rgamar jagorancin al-ummar kakansa(s), ya kuma bude jami’a ta farko a masallacin manzon Al..(s) a madina, inda yake karantar da fannoni ilmi masu yawa. Haka nan dansa Imam Sadik (a) ya zo ya bunkasa wannan jami’an a bayansa. Imam Bakir da Imam Sadik (a) sun sami damar haka ne a karshen mulkin bani Umayya , a lokacinda daular ta yi rauni. Muna taray al-ummar musulmi, musammam mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) da zagayowan ranar haihuwar Imam Bakir (a).
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 68 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Afrilun-1948M. Wasu kungiyoyin yan ta’adda na yahudawan sahyoniyya sun aiwatar da kisan kiya shi kan al-ummar Palasdinu mazauna garin Dir-Yasin a cikin yakunan Palasdinawa da suka mamaye. Wannan kisan kiyashi ya auku ne a dai dai lokacinda yahudawan suke shirye shiryen shelanta kafuwar haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin watan da ya biyu baya na wancan shekara. Munakhim Begin, Ishaq Shomir da kuma da kuma Devid Bengerion ne suka jagoranci wadan nan kungiyoyin yann ta’adda ukku don aiwatar da wannan kisan kiyashin, wanda ya tafi da rayukan mata da yaramasu yawa.