Apr 10, 2016 07:09 UTC

Yau Lahadi 22-Farvaddeen-1395 H.Sh=02-Rajab-1437H.K.=10-Afrilu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 997 da suka gabata a rana irin ta yau wato 02-Rajab-440H.K. Abu Raihan Biruni, daya daga cikin masani ilmin dabi’a da taurari ya rasu a birnin Gazne na kasar Afganistan a yanzu. Biruni ya tashi yana sha’awara karatun lissafi da kuma ilmin dabi’a. Bayan ya kore a kansu ya kuma neman wasu ilmomin wadanda suka hada da na taurari da goegraphia. Wani abu mai muhimmanci a cikin rayuwar Abu raihan shi ne, ya gano cewa duniyarmu ce take zagaya kanta da kanta sau daya a ko wace rana da yini, sannan take zagaye rana sau guda a shekara kafin masanan kasashen yamma irinsu galilio su gano hakan. Abu raihan yana da littatafai da dama wadanda suka hada da «آثار الباقیه»، و «الجواهر».

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Farvaddeen-1361H.SH. Gwamnatin JMI ta gano wani makirci na kokarin juyin mulki a kasar Iran don kawo karshen juyin juya halin musulunci a kasar. Tun bayan nasarar juyin musulunci a Iran ne makiya wannan juyin a cikin gida suke hada kai da na waje don ganin bayan juyin. A wannan karon wasu sojoji masu kishin kasa sun tseguntawa mahukunta wani shiri na juyin mulki wa gwamnatin JMI daga cikin gida, tare da samun kwakwarar hujjoji a kan wadanda suke jagorantar wannan makirshin. Daga cikin shirinsu dai akwai kasha dukkan masu fada a ji a cikin gwamnati, sannan daga baya su fito suna neman jininsu. Bayan bayyana wannan sirrin dai an kama dukkan wadan abin ya shafa kuma aka gurfanar da su a gaban koto.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Farvaddeen-1376H.SH. Bayan da wata kotu a kasar Jamus ta tuhumi wani jami’a babba a JMI da hannu wajen kisan wani ba Irane makiyan JMI da kwana guda dukkan gwamnatocin kasashen tarayyar Turai suka janye jakadunsu daga Tehran. Wannan kotun tare da hadin kai da HKI da kuma Amurka sun yi haka ne don maida JMI saniyar ware a cikin kasashen duniya. Amma a nata bangaren JMI ma ta janye dukkan jakadunta daga wadannan kasashe. Sai dai wannan halin bai jima ba sai na watanni 10, inda wadan nan kasashe daya bayan daya suka maida jakadunsu zuwa birnin Tehran.