Ko kunsan (23) Na 23 ga watan Farvaddeen shekara 1395 Hijira Shamsia.
Yau Litinin 23-Farvaddeen-1395 H.Sh=03-Rajab-1437H.K.=11-Afrilu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1183 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Rajab-254H.K. Limami na goma daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon Al..(s) wato Imam Aliyun Naqi dan Imam Mohammad Jawad (a) ya yi shahada. An haifi Imam Naqi, kuma Hadi a shekara ta 212 H.K. A Madina. Yana dan shekara 9 a duniya ya gaji mahaifin kan kujerar jagorancin Al-ummar kakansa. Imam Hadi (a) ya tarbiyantar da dalibai da dama a zamaninsa wadanda suka hada da Sayyeed Abdul-Azim al-hasani wanda hubbarensa yake garin Rai kusa da nan birnin Tehrai. Sai kuma manya manyan malamai wadanda suka hada da Ibnu Sikkeed Ahwazi, Isma’il Bin Mehron, Abu Hashim Jaafari, Jaafar bin Suhail da sauransu. Bayan shekaru 33 da jagoranci Imam hadi (a) ya yi shahada a rana irin ta yau a hannun jami’an sarki Mu’tazzu Billah , sarki na 13 daga cikin sarakunan Abbasiyawa wanda ya dasa masa guba a abincinsa da haka kuma ya yi shahada. A halin yanzu hubbarensa na birnin Samira na kasar Iraqi. Muna taya al-ummar musulmi juyayin wannan ranar.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 802 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Afrilun-1214M. Aka hai Roger Bacon wani masanin ilmin falsafa a kasar Britani. Da farko Bekon ya yi karatunsa ne a jami’ar Oxford. Bayan haka sai yashiga karantarwa. Wani abu mai muhimmanci a rayuwar Bacon shi ne fahintar cewaba’a samun ilmi sai ta hanyoyi biyu, wato jarrabawa da kuma hankali. Wannan fahintar ya sanya shi ne masani na farko wanda ya fara fito na fito da malaman kiristoci a lokacin wadanda suke da tsatsauran ra’ayi a akidunsu. Bacon ya ci gaba da wayar da kan mutane turai kan haka a duk tsawon rayuwarsa. Ya kuma rubuta littafai da dama wadanda suka hada da khulasa cikin ilmin kalam. Daga karshe ya rasu a ranar 25-Satumban-1294M yana dan shekara 80 a duniya.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Afrilun-1860M. Wani masanin ilmin kimiyyar sinadarai Ferdinand Carré dan kasar Faransa ya yi nasara kera na’ura mai samar da sanyi na farko a duniya. Aikin Ferdinand Carré dai ya kasance nasara babban a bangaren samar da sanyi wanda ba na dabi’a ba, kuma shi ne mataki na farko na samar da na’urorin sanyi wadanda suka hada da Firiji, wadanda ake amfani da su wagen adana abinci da magunguna don kada su lalace.