Ko kunsan (24) Na 24 ga watan Farvaddeen shekara 1395 Hijira Shamsia.
Yau Talata 24-Farvaddeen-1395 H.Sh=04-Rajab-1437H.K.=12-Afrilu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1279 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Afrilun-737M. Zaid bin Ali daya daga cikin yayan limami na ukku daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al…(s) ya fara yaki da sarakunan bani Umayya a birnin Kufa na kasar Iraqi. Mabiyansa ne ake kira shia zaidiyya. Yakin Zaidu bin Ali da sarakunan bani ummayya ya dauki tsawon shekaru biyu ana fafatawa. Amma daga karshe yayi shahada a hannun Yusuf Bin Umar thaqafi . Bayan haka ne wasu daga cikin mabiyansa suka koma kasar Yemen suka kuma assasa Daula ta shia zaidiyya a can. A halin yanzu rabin mutanen kasar Yemen mabiya wannan mazhabar ne. Kuma sune mabiya mazhabar shia mafi girma bayan shia Imamiyya. Banda su akwai mazhabar shia da ake kira shia Isma’iliyya.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 96 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Afrilun-1820M. Masana ilmin magani a kasar Faransa sun gano maganin cutar Maleria a karon farko wanda suka hada da sewan wata itaciya da ake kira Gene-gene. Masanan sun fidda ruwan wannan itaciyar daga sewarta suka kuma hada wani magani da ake kira –konin-. A ranar 12-Afrilun shekara 1820 ne aka fara amfani da wannan maganin a duniya. Ana samun itacen gene –gene a dazuzzukan kudancin Amurka da farko amma a halin yanzu ta watsu zuwa wasu kasashen duniya.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 66 da suka gabata a rana irin ta yau wato 4-Rajab-1371H.K. Aya Amini Amuli daya daga cikin manya manyan malaman Shia a yankin Jabal Amil na kasar Lebanon ya rasu. An haifi Aya. Amin Amuli a shekara ta 1284 H.K. kuma ya fara karatun sharer fage a gida. Aya. Amin Amuli yana dan shekara 24 ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kamala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin. Bayan kamala karatu ya shiga karantarwa da kuma wallafe wallafe. Daga cikin littafan da ya rubuta akwai littafi mai suna اعیان الشیعه inda ya kawo tarjamar malaman mazhabar shia a duk tsawon tarihi.