Ko kunsan (26) Na 26 ga watan Farvaddeen shekara 1395 Hijira Shamsia.
Yau Alhamis 26-Farvaddeen-1395 H.Sh=06-Rajab-1437H.K.=14-Afrilu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 954 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Rajab-483H.K.Hassan Sabbah daya daga cikin shuwagabannin shia Isma’ilia a nan kasar Iran ya kwace iko da wani gari da ake kira Alamut kusa da garin Qazwin a arewacin kasar Iran. Banda haka Sabbah ya kwace wasu garuruwa da dama a yankin, ya kuma kafa daular Isma’ilawa. Daga cikin many manyan mutanen da ya sami damar jawosu zuwa cikin daularsa dai sun hada da Khoja Nizamul-Mulk. Daular Isma’iliyya karkashin sarakunan salujukiyyawa ta wanzu har zuwa shekara 654H.K. a lokacinda mongolawa suka kutsa cikin daular musulunci.
02-Masu sauraro ko kun sann cewa shekaru 890 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Afrilun-1126M. Aka haifi Ibn Rushdi babban malamin addini kuma masanin ilmin irfani ko tasawwuf a kasar Andulus, wanda a halin yanzu wani bangare ne na kasar espania. Mahaifi da kuma kakakn Ibnu Rushdi sun kasance alkalai. Ibn Rushdi yana matashi ya yi zurfi a ilmomi da dama. Wannan ya ja hankalin sarakunan andulus na lokacin inda suka sanya shi alkalin alkalai a babban birnin daular wato Qurtab. Ibn rushdi ya rubuta littafai da dama wadanda suka hada da «کتاب الکلیات» cikin ilmin magunguna da kuma .«تهافُت التهافت»، . Ibnu Rushdi ya rasu a shekara ta 595 H.K.
3-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Afrilun-1988M. gwamnatin tarayyar Soviet ta lokacin ta rattaba hannu kan wata yerjejeniya wacce ta bukaci tarayyar Soviet ta janye sojojinta daga kasar Afganistan, wacce ta mamaye tun watab decenban shekara 1979M. Kafin haka dai mutanen kasar Afganistan sun dauki makamai don korar sojojin mamaya na tarayyar Soviet daga kasar. Har’ila yau a wani bangare kuma kasar Amurka wacce ta ga cewa mamayar kasar Afganistan da tarayyar soviet tayi wata barazana ce ga bukatunta a yankin ta tallafawa mujahidin kasar Afganistan don ganin Soviet ta fice daga Afagnistan. Daga karshe dai shugaban tarayyar Soviet na lokacin Michel Gobachev ya bada umurnin ficewar sojojin T. soviet daga kasar Afganistan a cikin watan Febrerun shekara 1989.