Ko kunsan (27) Na 27 ga watan Farvaddeen shekara 1395 Hijira Shamsia.
Yau Jumma’a 27-Farvaddeen-1395 H.Sh=07-Rajab-1437H.K.=15-Afrilu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 104 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Afrilun-1912M. Jirgin ruwan daukar fasinja mafi girma wanda aka taba ginawa zuwa lokacin mai suna tatanic ya yi hatsari a cikin tekun Atlantic a lokacinda yake kan hanyarsa ta zuwa birnin New York na kasar Amurka daga mazauninsa da ke kasar Britania. Tatanic yana dauke da fasinjoji 2207 a lokacinda ya yi karo da dutsen kankara a cikin taken. Kuma dukkannin fasinjojin jirgin sun halaka in banda mutum 705. Wanna shi ne hatsarin jirgin ruwam fasinja mafi muni a lokacin.
02-Masu sauraro ko kun sann cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Afrilu-1982M. An zartar da hukuncin kisa kan Khalid Islam Buli wani sojan kasar Masar wanda ya kasha shugaban Anwar Sadad a wani fareti na tunawa da yakin watan Octoba na shekara ta 1973. Bayan da shugaba Anwar sadat ya rattaba hannu kan yerjejeniyan sulhu ta Camp Devid ta neman zaman lafiya da HKI, hakan ya fusata kasashen larabawa da musulmi da dama. Islam buli ya hada kai da masu ra’ayin jihadi a kasar Inda a lokacinda motarsu take wucewa gaban shugaba Sadat ya sauka tare da wasu mutanensa suka kuma budewa sadat wuta suka kasha shi. Bayan haka ne aka kama Islambuli suka gurfanar da shi a gaban kotu suka kuma bindigeshi a rana irin ta yau.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 22 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Afrilun-1994M. Wakilan kasashen duniya da dama suka rattaba hannu kan yerjejeniyar kafa kungiyar kasuwanci ta duniya wato W.T.O a wani taron da aka gudanar a kasar Morocco. An kara kungiyar kasuwanci ta duniya ta farko ne a shekara 1947 bayan yakin duniya na biyu tare da kasashe 23, wacce kuma ake kira GATT. An sake irin wannan taron a shekara 1986 a kasar Urugay. Amma a shekara 1994 kasashen duniya da dama suka halarcin taron GAAT a morocco suka kuma sauya sunan kungiyar zuwa WTO. Bayan sun cimma yerjejeniya kan rage kudaden fito tsakanin kasashen duniya don samar da sakin shiga da fita da kayakin kasuwanci.